You are here: HomeAfricaBBC2023 05 30Article 1776806

BBC Hausa of Tuesday, 30 May 2023

Source: BBC

Chelsea ta nada Pochettino sabon kocinta

Mauricio Pochettino Mauricio Pochettino

Chelsea ta sanar da nada tsohon wanda ya horar da Tottenham da Paris St-Germain, Mauricio Pochettino a matakin sabon kocinta.

Dan kasar Argentina, mai shekara 51, zai fara aiki a Stamford Bridge ranar 1 ga watan Yulin 2023 kan yarjejeniyar kaka biyu da cewar za a iya tsawaitata da kaka daya.

Kocin rikon kwarya, Frank Lampard ya kai Chelsea mataki na 12 a teburin Premier League, mataki mafi rashin kokari tun bayan shekara 25.

Chelsea ta ce Pochettino ya zama a cikin masu zawarcin aikin, kuma shi kadai ta gayyata tattaunawa da mahukunta, wanda yake da kwarewa.

Zai yi aiki tare da daraktan wasannin kungiyar, Paul Winstanley da kuma Lawrence Stewart.

Pochettino shine na shida da Chelsea ta dauka cikin kaka biyar, ciki har da korar Thomas Tuchel da Graham Potter a farkon kakar nan, daga baya ta dauki Lampard rikon kwarya.

Haka kuma Pochettino ne na hudu karkashin sabon shugaban Chelsea, Todd Boehly, bayan da ya karbi kungiyar a watan Yulin bara.

Chelsea ta fuskanci kalubalen tamaula a kakar nan, wadda Manchester City ta fitar da ita a FA Cup da kuma League Cup.

Haka kuma Real Madrid ce ta fitar da Chelsea a gasar Champions League na bana, yayin da kungiyar ta kasa samun gurbin shiga gasar zakarun Turai ta badi.