You are here: HomeAfricaBBC2023 05 30Article 1776812

BBC Hausa of Tuesday, 30 May 2023

Source: BBC

Batun tsaro da tattalin arziki zan sa gaba a Kaduna — Uba Sani

Sabon gwamnan jihar Kaduna sanata Uba Sani Sabon gwamnan jihar Kaduna sanata Uba Sani

A Litinin ne ake rantsar da shugaban kasa da kuma sabbin gwamnoni a jihohin Najeriya 28.

Shiyyar arewa maso yammacin Najeriya dai sabbin gwamnoni bakwai za a rantsar.

Jihohin da ke cikin wannan shiyyar sun hada da Kano da Kaduna da Jigawa da Kebbi da Sokoto da Zamfara da kuma Katsina.

A jihar Kaduna, za a iya cewa tazarcen mulki ne al’ummar jihar zasu gani, kasancewar jam’iyyar APC ce zata ci gaba da jan zarenta.

Tun a karshen makon da za a rantsar da sabon gwamnan jihar ne, gwamna mai barin gado Malam Nasir El Rufai, ya mikawa zababben gwamnan jihar sanata Uba Sani, kundin bayanan sha’anin mulki wanda kwamitin karbar mulki ya gabatar.

BBC ta tuntubi sabon gwamnan na Kaduna kan abubuwan da al’ummar jihar za su gani bayan rantsar da shi, kuma ya bayyana abubuwa da dama, amma ya fara ne da batun tsaro.

Ya ce, ‘’ Duk abin da ya shafi sha’anin tsaro na al’ummarmu da abin da ya shafi dukiyarsu dole mu tsaya tsayin daka mu ga mun kare su, sannan batun bunkasa tattalin arziki saboda mutane na cikin wani yanayi.”

Sanata Uba Sani, ya ce za kuma su yi ayyuka na ci gaba a kauyuka da bunkasa ilimi da hanyoyi da kuma inganta sana’ar al’umma.

A jihar Kano kuwa, tuni shirye-shirye suka kammala a filin wasa na Sani Abacha da ke birnin don rantsar da sabon gwamnan jihar injiniya Abba Kabir Yusuf, tare da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam, wadanda suka yi nasara a zabukan da suka gabata.

Wannan rana dai muhimmiya ce ga Kwankwansawa masu jar hula, inda za su sake karbar mulki, bayan sun shafe tsawon shekaru suna zaman adawa da gwamnatin da suka kafa tun da farko a 2015, amma daga bisani suka raba gari da Dr. Abdullahi Umar Ganduje, inda aka shiga zazzafar adawa da juna.

Jami’an tsaro musamman ‘yan sanda sun ce sun yi kyakkyawan shirin samar da tsaro ya yin wannan bikin karbar mulki.

Suka ce sun jibge jami’an tsaro a mihimman wurare don tabbatar da doka da oda, Sannan kuma sun gargadi masu neman haddasa fitina da su yi kuka da kansu.