You are here: HomeAfricaBBC2023 05 30Article 1776755

BBC Hausa of Tuesday, 30 May 2023

Source: BBC

Juventus ta cimma matsaya da hukumar ƙwallon Italiya

Gidan Juventus, filin wasa na Turin Gidan Juventus, filin wasa na Turin

Hukumar kwallon kafar Italiya ta sanar da cimma yarjejeniya da Juventus don kawo karshen zargin badakalar da ta shafi biyan 'yan wasa albashi.

Juventus ta tsaya tsayin daka domin kamo bakin zare kan takaddamar da ke tsakaninta da hukumar, domin ta samu damar fuskantar kakar badi cikin shiri.

Cikin yarjejeniyar da aka kulla, Juventus ta amince za ta biya tarar dala 790,000, kuma babu batun daukaka kara a kotun kararrakin wasanni.

Haka kuma ba za a kara kwashe wa Juventus maki ba bayan da aka karbe maki 10 har karo biyu kan zargin badakalar cinikayyar 'yan wasa.

Saura wasa daya a karkare kakar Serie A ta bana, kuma da wannan hukuncin Juventus tana ta bakwai a teburi da maki 59. Watakila ta samu gurbin Europa Conference League a badi.

Sai dai wasu jaridun Italiya na cewa watakila Juventus ta kasa buga gasar zakarun Turai a badi idan hukumar kwallon kafar Turai ta yi nata hukuncin.

Ana tunanin akwai yiwuwar UEFA ta kwashe wa Juventus maki da zarar an kammala kakar bana, abin da zai sa kungiyar ta kasa buga Europa Copnference League a badi.