You are here: HomeAfricaBBC2023 05 23Article 1772420

BBC Hausa of Tuesday, 23 May 2023

Source: BBC

Masarautar Birtaniya ta yi watsi da roƙon mayar da gawar yariman Habasha gida

Yarima Alemayehu Yarima Alemayehu

Fadar Masauratar Ingila ta ƙi amincewa da sabbin kiraye-kirayen mayar da gawar Yariman Habasha gida, wanda aka binne a gidan masarautar Ingila ta Windsor Castle a karni na 19.

Yarima Alemayehu ya isa Birtaniya a matsayin maraya, ɗan shekara bakwai bayan mahaifiyarsa ta rasu a kan hanyar zuwa Birtaniyar.

"A matsayinmu na iyalansa kuma ƴan Habasha muna buƙatar gawarsa saboda ba a Birtaniya aka haife shi ba," A cewar ɗan'uwansa Fasil Minas yayin hira da BBC.

Ya ƙara da cewa "bai kamata a binne shi a Birtaniya ba".

Bayan an kai shi ƙasar, Yariman ya mutu ne a shekarar 1879 yana ɗan shekara 18 bayan fama da cutar wahalara numfashi, sannan Sarauniyar Ingila ta wancan lokacin, Victoria ta buƙaci masarautar ta taimaka masa da kuɗin jinya.

Sai dai a wata takarda da ya aike wa BBC, mai magana da yawun fadar Buckingham ya ce tono gawar Yariman za ta shafi wasu kaburbura a maƙabartar ta St George Chapel da ke fadar ta Windsor Castle.

"Da kamar wuya a iya tono gawarsa ba tare da ya shafi ɗimbin sauran mamata da ke kwance a wurin ba," A cewar fadar.

Sanarwar ta ƙara da cewa hukumomin makabartar suna girmama bukatar ta tono Yarima Alemayehu amma kuma suna da hakkin kare martabar mutane da suka rasu".

Ta ƙara da cewa a baya hukumomin makabartar sun amince tawagogin Habasha da dama su ziyarci makabartar da yariman yake kwance.

Yarima Alemayehu ya samu kansa a Burtaniya ne a shekarun farko na rayuwarsa sakamakon rashin aiki da diflomasiyya.

A yuƙurinsa na ƙarfafa masarautarsa a shekarar 1862, mahaifin Yariman, sarki Tewodros na biyu ya buƙaci haɗin gwiwa da Burtaniya, to amma bai samu martanin wasiƙun da ya aike wa sarauniya Victoria ba kan wannan batun.

Bayan ya harzuƙa da rashin martani daga Birtaniyar sai sarkin ya ɗauki mataki da kansa inda ya kama wasu Turawa ciki har da ƴan asalin Birtaniya.

Wannan matakin ya jawo an aika sojojin Birtaniya da India 13,000 su ceto mutanen da ya kama.

Cikin tawagar sojojin har da jami'an ɗakin adana kayan tarihi na Birtaniya.

A watan Afrilun shekara ta 1868 sojojin sun yi wa dutsen da sarki Tewordoros yake ƙawanya a yankin Maqdala a arewacin Habasha kuma cikin sa'o'i kaɗan aka ci sarkin da yaki.

Sarkin ya yanke shawarar ya kashe kansa maimakon ya zama fursunan Birtaniya, matakin da al'ummarsa ke ganin bajinta ce.

Bayan yaƙin, sojojin Birtaniya sun sace dubban kayan tarihin gargajiya da na addini waɗanda suka haɗa da kambin zinare da litattafai da sarƙoƙin wuya da tufafi kala-kala.

Masana tarihi sun ce sai da sojojin suka yi amfani da gwamman giwaye da kuma jakuna wajen kwashe kayan da suka sace zuwa yankunan Turai da dama.

A yanzu haka dai wasu daga cikin kayan na wurare daban-daban a gidajen adana kayan tarihi da kuma dakunan ajiye litattafai a Turai.

Sojojin na Burtaniya sun kuma kama Yarima Alemayehu da mahaifiyarsa sarauniya Tiruwork Wube.

A cewar sojojin, sun ɗauke su ne don kar maƙiya sarkin su kama su ko kuma su kashe su, haka nan ma mawallafin littafin nan na "The prince and Plunder" Andrew Heavens, ya jaddada hakan a wani bayani kan abin da ya faru da Alemayehu.

Bayan ya isa Birtaniya a watan Yuni 1868, halin da Yariman yake ciki a matsayinsa na maraya ya sa sarauniya Victoria ta tausaya masa matuƙa, sai ta nemi su gana a gidan hutunta da ke Isle Wight da ke kudancin Ingila.

Sarauniyar ta kuma amince ta taimaka masa da kudi sai kuma ta bayar miƙa harkar kula shi ga Kyaftin Tristram Charles Sawyer Speedy, mutumin da ya raka Yariman zuwa Birtaniya daga Habasha.

Da farko dai sun zauna ne a garin Isle Wight sannan daga bisani Kyaftin Speedy ya zagaya da shi sassan duniya daban-daban ciki har da India.

To amma an yanke shawarar cewa yariman ya shiga makarantar boko.

Sai kuma aka shigar da shi makarantar gwamnatin Birtaniya ta Rugby amma bai ji daɗinta ba. An mayar da Yariman makarantar soji ta Royal Military College da ke Sandhurst inda aka riƙa cin zarafinsa.

An bayyana cewa ya riƙa jin yana son ya koma gida amma aka ƙi bashi dama.

"Na san irin hali da ya shiga, na kuma fahinci irin halin da ya tsinci kansa a ciki saboda an nesanta shi da Habasha, an nesanta shi da ƙasar baƙaƙen fata har ya zama kamar ba shi da asali," kamar yadda Abebech Kasa ta shaida wa BBC.

Daga ƙarshe dai an riƙa azabtar da Alemayehu a wani gida a birnin Leeds.

Cutar sanyin haƙarƙari ta kama Yariman sannan ya ƙi karɓar magani saboda ya na tunanin guba aka saka mishi.

Bayan shafe shekara goma yana gudun hijira, Yariman ya mutu a shekarar 1879 ya na ɗan shekara 18.

An yi ta wallafa batun mutuwarsa a jaridun Birtaniya kuma sarauniya Victoria ta kaɗu matuka da mutuwar.

Bayan samun labarin, ta rubuta saƙon jimami a cikin littafin kundinta.

"Na ji takaici da kuma kaɗuwa da jin labarin rasuwar Alemayehu ta hanyar telegram da safiyar nan, yaro ne mai hankali".

"Abin baƙin ciki ne saboda ya rasu shi kaɗai a wata ƙasa ba tare da ko da ɗaya daga cikin ƴan uwansa ba," a cewar sarauniyar.

"Rayuwarsa ba ta yi daɗi ba, saboda tana cike da wahalhalu daban-daban, sannan ya riƙa tunanin mutane suna yi mishi kallon baƙin mutum.....kowa ya kaɗu matuƙa da mutuwarsa".

Sannan sai sarauniyar ta shirya masa jana'iza a fadar Windsor Castle.

Buƙatun mayar da gawar Yariman dai ba sabbon abu ba ne.

Ko a shekarar 2007, shugaban Habasha Girma Wolde-Giorgis ya rubuta wa Sarauniya Elizabeth ta biyu wasiƙa kan buƙatar a mayar da gawar Yariman to sai dai haƙarsa ba ta cimma ruwa ba.

"Muna buƙatar a dawo mana da shi. Ba mu son gawarsa ta ci gaba da kasancewa a ƙasar waje," A cewar Ms Abebech.

"Ya yi rayuwa mara daɗi. Idan har na tuna da shi ina kuka. Idan har suka dawo mana da gawarsa zan ji kamar a raye ya dawo gida."

Abebech tana sa ran Sarki Charles III zai amince da buƙatar tasu.

"Mayar da kayan da aka sace zai iya kawo sasanci a cewar Farfesa Alula Pankhurst, wani ƙwararre a fannin nazarin dangantaka tsakanin Burtaniya da Habasha.

Farfesan ya na ganin mayar da gawar Yariman za ta iya kasancewa wata hanya da Birtaniya za ta tuna abin da ta aikata a baya.