You are here: HomeAfricaBBC2023 05 23Article 1772426

BBC Hausa of Tuesday, 23 May 2023

Source: BBC

Yarjejeniyar tsagaita wuta na gab da rugujewa a Sudan

An kashe daruruwan mutane tun bayan da aka fara fada a Sudan An kashe daruruwan mutane tun bayan da aka fara fada a Sudan

An samu rahotanin da ke cewa an kai karin hare hare ta sama da kuma fada a Sudan wanda ke kawo cikas ga fata na baya-baya nan kan shirin tsagaita wuta a Sudan da ke fama da rikici.

Sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon kwanaki 7 a hukumance ta fara aiki ne da misalign karfe tara da minti arbain da biyar agogon gida watau karfe 19:45 agogon GMT.

Sai dai shaidu sun yi magana akan karin tashin hankali a birnin Khartoum da sauran wurare.

A cikin Makoni biyar da suka gabata ne fada ya barke tsakanin manyan hafsoshin sojin kasar wadanda ke rikici kan mulki.

Yunkurin da aka yi a baya na kawo kawo karshen rikicin a arewa maso gabashi Afrika ya rika tangal-tangal ko kuma ma ya ruguje.

An sake samun kyakkyawan fata ga sabuwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta, wacce ta biyo bayan tattaunawar da Saudiyya da Amurka suka shirya.

Sabuwar yarjejeniyar za ta kasance karkashin wani tsari na masu sa ido,’’ a cewar sanarwar da Amurka da Saudiyya suka fitar a ranar Asabar, wacce ta amince da gazawar da aka samu a baya wajan samar da zaman lafiya.

Sai dai dakarun rudunar kar ta kwana ta RSF sun fitar da wani sako sa’oi kadan kafin yarjejeniyar ta fara aiki.

An nadi muryar Janarar Mohamed Hamdan Dagalo da aka fi sani da Hemedti yana isar da sako yana cewa dakarunsa ba za su ja da baya ba "har sai mun ga bayan wannan juyin mulki”

Shaidu sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an gwabza kazamin fada a arewacin Khartoum mituna kadan bayan sabuwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta baya baya nan ta soma aiki a arewacin birnin da kuma hare hare ta sama a gabashi.

Haka kuma farar hula sun shaida wa kamfanin Reuters cewa sun ji karar harbe -harbe a Omdurman da Bahri. Sai dai ba su bayar da rahoto a kan an sabawa yarjejeniyar ba.

A ranar 15 ga watan Afrilu ne rikici ya barke a birnin Khartoum bayan kwanakin da aka kwashe ana zaman dar-dar yayin da aka sake tura dakarun RSF zuwa sassan kasar a wani mataki da sojojin kasar ke ganin barazana ce.

Rikici tsakanin Janarar Dagalo da hafsan hafsoshin sojin kasar Janarar Abdel Fattah al-Burham wanda shi ne ya ke rike da ragamar mulki tun bayan da aka hambarar da shugaba Omar al Bashir daga mulki 2019.

An kashe daruruwan mutane tun bayan da aka fara fada kuma Majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewa lamura na kara tababbarewa a kasar da ke da dimbin mutane da suka dogara akan kayan agaji kafin barkewar rikicin.