You are here: HomeAfricaBBC2023 05 12Article 1765448

BBC Hausa of Friday, 12 May 2023

Source: BBC

Watakila Manchester United ba za ta dauki Kane ba, Chelsea ma ta dakata daukar Osimhen

Harry Kane Harry Kane

Manchester United na fargabar watakil su gagara dauko mai kai hari na kungiyar Tottenham Harry Kane a kakar nan, ya yin da Spurs ke son kaftin din Ingilar mai shekara 29 ya ci gab ada zama duk da shekara guda ta rage a kwantiraginsa da kungiyar. (Mirror)

Shugaban La Liga Javier Tebas ya ce tafiyar dan wasan tsakiya na Sifaniya Sergio Busquets daga Barcelona somin tabi ce ga kulab din na Sifaniya ya sake daukar dan wasan gaba na Argentina Lionel Messi mai shekara 35, wanda kwantiraginsa da PSG zai kare a kakar nan. (Cadena COPE - in Spanish)

Chelsea ta dakata kan daukar dan wasan Napoli Victor Osimhen, sayan dogon nazarin zai yi wuya ta iya kammala cinikin dan wasan Najeriyar mai shekara 24 a kakar nan.(Football Insider)

Dan wasan tsakiya a kan gaba a Belgium Romelu Lukaku, mai shekaru 29, zai koma daga Chelsea daga zaman aron da ya ke yi a Inter Milan a kakar wasa, ana kuma tattaunawa da sabon kocin Blues Mouricio Pochettin, da batun atisaye gabannin kakar wasa ta gaba da kuma rawar da zai taka nan gaba a kungiyar. (Mirror)

Pochettino na son Chelsea ta sake duba batun kwantiragin dan wasan tsakiya na Ingila Mason Mount mai shekara 24, wanda kwantiraginsa da Blues ke gab da karewa a karshen kakar wasa mai zuwa. (Standard)

Aston Villa na tattauna domin daukar dan wasan tsakiya na Sporting Lisbon midfielder Manuel Ugarte, ya yin da dan wasan na Uruguay ke samun goron gayyata daga kungiyoyin Liverpool da Chelsea na shiga cikinsu domin taka leda. (Football Transfers)

Eja din Ugarte ya ce akwai kungiyoyi da dama da ke nuna sha'awar daukar dan wasan, wanda kwantiraginsa da Sporting Lisbon ke karewa a kakar nan. (O Jogo - in Portuguese)

Arsenal na zuba ido kan Diaby da fatan daukarsa a watan Junairu, sannan alamu sun nuna zai yi kasuwa a kakar wasa (Standard)

Everton ta nuna sha'awar daukar dan wasan Southampton, kuma mai tsaron gida na Ghana Mohammed Salisu, mai shekara 24, da kammala batun komawar shi kungiyar a kakar wasa. (Football Insider)