You are here: HomeAfricaBBC2023 05 09Article 1763636

BBC Hausa of Tuesday, 9 May 2023

Source: BBC

An samu tsaiko a yaƙi da mutuwar masu juna biyu da jarirai - MDD

Shekaru takwas kenan ba a samu ci gaba ba wajen rage mace-macen mata masu juna biyu Shekaru takwas kenan ba a samu ci gaba ba wajen rage mace-macen mata masu juna biyu

Wani rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya nuna cewa an shafe shekara takwas ba tare da wani ci-gaba ba a ƙoƙarin da duniya ke yi na rage matuwar mata masu juna biyu da jarirai.

Hakan ya faru ne, sakamakon raguwar hidimar da ake yi ta inganta rayuwar mata masu juna biyu da jirarai.

Rahoton ya ce mata da jarirai miliyan huɗu da dubu ɗari biyar ne ke mutuwa a kowace shekara sakamakon rashin kulawa.

Haka kuma rahoton ya bayyana cewa shekara takwas kenan, ƙoƙarin da ake yi na rage matuwar mata masu juna biyu, da matsalar ɓari da mutuwar jarirai bai samu wani ci gaba ba.

Tun shekarar 2015 zuwa yanzu jarin da ake zubawa a fannin inganta lafiyar iyaye mata da jariran ya ragu, kamar yadda rahoton ya nuna.

Alƙaluman rahoton sun nuna cewa mata da jarirai miliyan huɗu da dubu dari biyar ne ke mutuwa a kowace shekara.

Abin da ke nufin cewa cikin kowace daƙiƙa bakwai mutum guda na rasa ransa.

Rahoton ya kuma nuna cewa cututtuka ko abubuwan da ke haddasa mutuwar, abubuwa ne da za a iya kauce mu su, ko magance su, idan an mayar da hankali da bayar da kulawar da ta dace.

Dakta Anshu Banaji, Darakta a Hukumar Lafiya ta Duniya ya ce annobar korona ta janyo koma-baya sosai wajen samar da kulawa ga mata masu juna biyu da jarirai.

Kuma a cewarsa matuƙar duniya na son samun sauyi, to wajibi ne a sauya yadda ake tunkarar lamarin.

Don haka akwai buƙatar a kara zuba jari a harkar inganta lafiyar mata da jarirai.

Duk da cewa annobar korona ta shafi ƙasashen duniya baki-ɗaya, rahoton ya ce akwai bambanci dangane da girman illar da ta yi daga ƙasa zuwa ƙasa.

Don haka ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi ko masu fama da talauci sun fi sauran ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki galabaita.

Rahoton ya ce tun a shekarar 2018, kuɗin da ake kashewa wajen inganta lafiyar mata da jarirai ya ragu a kashi uku ciki huɗu a ƙasashen Afirka da ke kudu da hamadar sahara.

Misali ƙasa ɗaya cikin 10 ne a fiye da ƙasashe 100 da aka gudanar da binciken ke samun isassun kuɗin inganta lafiyar mata da jariran, a cewar rahoton.

Binciken ya yi gargaɗin cewa ƙarancin kuɗi na inganta lafiya a matakin farko na shafar makomar rayuwa al'umma, musamman yadda matsalar ke haddasa mutuwar yara 'yan ƙasa da shekara biyar da haihuwa a duniya.

Game da mafita kuwa, rahoton ya jaddada cewa akwai bukatar a inganta lafiyar mata da jarirai ta hanyar samar mu su da muhimman abubuwan da ake buƙata a farashi mai sauƙi.

Da kuma samar da ƙwararrun masu kula da lafiyarsu da kuma kayan aiki mai nagarta.

Haka kuma, kamar yadda binciken ya nuna, za a samu sauƙi matuƙa idan aka kawar da wasu miyagun al'adu da camfe-camfe.