You are here: HomeAfricaBBC2023 05 09Article 1763183

BBC Hausa of Tuesday, 9 May 2023

Source: BBC

“Ina ganin budurwata ta mutu ne sakamakon kaciyar da aka yi mata”

Hoton alama Hoton alama

Saliyo ta fi kowace kasa a Africa yawan mata da aka yi musu kaciya, abin da a mafi yawan lokaci yakan haddasa musu bala’i.

BBC Africa Eye ta tattauna da wani mutum da yake da yaƙinin cewa budurwarsa ta mutu ne sakamakon kaciyar da a ka yi mata.

Fatmata Turay na da shekara 19 da haihuwa a lokacin da mahaifiyarta ta bukace ta ta ziyarci ƙauyensu.

An ƙaddamar da ita cikin ƙungiyar al’ummar Bondo, wanda al’ada ne da aka kwashe shekaru da dama a na yi kuma ya kushi kade-kade da raye-raye inda ake shirya ‘yan mata su zama manyan mata.

Bayan sa’o’i 36, Fatmata ta mutu.

Daga ranan 18 ga watan Agustan shekara ta 2016 da aka yi jana’izar ta, saurayin ta, kuma dan jarida Tyson Conteh y afara yin bidiyo.

A wani bidiyo da ya yi daga baya, ya kalli kyamara ya yi bayanin abin da ya tunzura shi ya yi bayanin abubuwan da ke faruwa.

“Ina son in yi amfani da wannan fim din, wanda ke da muhimmanci a gare ni, in zakulo batun mahawara. Fatmata ba ta son ta ga wata yarinya ko mata ta sake mutuwa. Burin ta ke nan”

Ya ce Fatmata na masa magana a mafarki, kuma ta bukaci ya zakullo gaskiyan batun mutuwar ta kuma ya kawo karshen kaciyar mata.

Kaciyar mata shi ne yanke wani bangaren al’uran mace ko kuma debe shi baki daya.

Hukumar kula da yawan jama’a na majalisar dinkin duniya ta ce kasashe 92 ke da wannan al’adar, amma an fi yin sa ne a yankunan Afrika da kuma gabas maso tsakiya.

A kasashe kamar su Somalia, da Sudan da Djibouti akwai wani salon kaciyar da a ke yi mai suna “infibulation” inda a ke yanke lebban al’uauran mata sai a yi amfani da su wurin neman a shafe tsagun al’auran baki daya, sai da a bar wani dan bamgare don fitar fitsari da jinin al’ada. Idan mace ta yi aure, sai an sake yi ma ta tsau kafin mijin ta ya kusance ta.

Kaciyar mata ba ta da wata fa‘ida ta fannin lafiya. Hukumar lafiya ta Duniya ta yi gargadin cewa ta na iya janyo mastalolin fitsari, da na al’ada ga mata wanda ke iya haifar da matukar damuwa wurin haihuwa ha rya kai ga mutuwa.

A kasar Sierra Leone, na kiyasta kimanin kashi 83 na mata da ke tsakanin shekaru 15 zuwa 49 an yi musu kaciya.

Daya daga cikin dalilan yin kaciyan shi ne a rage wa mata sha’awa. Idan an yanka su, a na tunanin zai taimaka wurin kamun kai kuma ya tabbatar da sun tsaya ga mazajen su bayan sun yi aure.

“Macen da ba a yanka ba ta fi wacce a ka yanka sha’awa. Shi ya sa mu ke rage musu jin sha’awar.” A cewan Aminata Sankoh, wata mai aikin yi wa mata kaciya da a ka fi sani da soweis a kasar Sierra Leone.

‘Sai da na yi mako daya kafin in yi fitsari’

Conteh ya samu daman daukan hotunan bukin mata na kungiyar al’aumman Bondo, al’ada mai dogon tarihi.

Buki ne da ake yin sa inda manyan matan al’umman ke koya wa ‘yan mata al’adun zama matan aure da kuma uwaye

Abu ne da ya zame dole kuma an saba da shi.

Amma cikin abubuwan da ake gudanarwa a bukin har da kaciya. Ba a baiwa Conteh daman daukan hoton ba

“A al’adar mu, mutanen mu sun dade su na shiga wannan kungiyar al’umman” a cewar Ngaima Kamara wata gagarumar soweis.

“idan ba ki shiga ba, za ki ji kunyar yin wanka da ni a rafi, idan na wuce ki, ba zan yi mi ki magana ba. Idn mu ka hadu a wani wuri ina iya fada mi ki cewa ba na magana da wace ba a yanka ta ba. Kamar ba ki da lafiya ”

A wannan daftarin, Conteh, ya yi bayani abin da ya faru da Fatmata, kwana daya bayan ta dawo daga bukin Bondo.

“Mun ga gawar ta a kwance kan tabarma, a kofar gida a kasa. Kuma na lullube ta da farin kyalle” a cewar sa.

“Ka na ganin jin na fita. Ka na gani akwai jini kuma mun yi la’akari da cewa ta mutu ne bayan an yi yanka ta ne a bukin al’umman Bondo”

‘Yan Sanda sun isso sai aka tafi da gawar Fatmata wurin ajiyan gawawwaki a Makeni.

An kama mahaifiyar ta da Soweis din da ta yi aikin.

Bayan kwana shida, Dokta Simeon Owizz Koroma, ya gudanar da bincike kan gawar ta.

A wurin har da Dr Sylvia Blyden ministar kula da jama’a da harkokin mata da yara

Dr Blyden na goyon bayan manyan matan da ke son a yi musu kaciya amma ta na yaki da tursasawa kananan yara mata.

A wani jawabi da ta yi, ta yi bayanin sakamakon binciken gawar da a ka yi kuma ta ce ba kaciyar ce ta kashe ta ba. An saki Soweis din da mahaifiyar Fatmata.

Conteh ba yi binciken ko an yi rufa-rufa kan mutuwar budurwarsa domin a kare al’umman Bondo. Dr Blyden ta dage ka cewa ba za ta danne gaskiya don ta katre mutuncin al’umman Bonbdo ba.

Rugiatu Turay, wace babu ‘yan uwantaka tsakanin ta da Fatmata, ita ce mataimakiyar Dr Blyden a lokacin kuma ta dade ta na yaki ta al’adan kaciyar mata.

She founded and runs the Amazonian Initiative Movement, an organisation in Sierra Leone focused on ending FGM.

Ta kaddamar da kungiyar Amazonian Initiative Movement, wata kungiya a kasar Sierra Leone da ke yakin kawo karshen kaciyar mata.

Ta ce ta taki sa’an tsira bayan an yi ma ta kaciya ta na da shekaru 11

"Plenty people have died. We know, we all know. We should be honest,' she said.

“Mutane dayawa sun mutu. Mun sani, dukan mu mun sani. Mu fadi gaskiya” Ta ce.

„Na kusa mutuwa. Idan zan yi fitsari. Sai da na yi mako daya kafin na iya yin fitsari. Mako daya. Ko bayan an gama komai. Al’aura ta ta kumbura.”

Bondo za ta kare

Ms Turay ta tuhumi abin da ya sa Dr Blyden ta halarci wurin binciken gawar.

“Menene za isa a bar minsta ta shiga wurin ajiyan gawawwaki ta yi binciken gawa? Ko da kuwa likita ce, babu abin da za ta yi a wurin”

„Ta tsaya tare da Soweis din. Ta riga ta nuna son kai. Mun na da yakinnin cewa na canza sakamakon da ba a yarda mun gani ba. Abin da mu ka yarda ke nan. Bai kamata mu yi musayar rayukan mata da kuri’u ba”

Dr Blyden, ta musanta cewa ta yi magana kan mutuwar Fatmata a bayyane amma ta na kan bakan ta na cewa ba kaciya ce ta kashe ta ba, ta ce binciken gawar da a ka yi ya yi daidai da yanayin lafiyar Fatmata.

Ta ce duk wani zargin da a ke yi na cewa an yi rufa-rufa kan mutuwar ba gaskiya ba ne, ta kara da cewa binciken gawar an yi ta ne a idon ‘yan uwan ta, da kungiyoyin kiyaye hakkin mutane, da ‘yan sanda da kuma ma’aikatan lafiya. Ta yi bayyanin cewaaikin ta ne a mtsayin ta ta minista ta halarci wurin binciken gawar, kuma ba don siyasa ta halarci wurin ba.

BBC Africa Eye ta tunkari Dr Owizz da zargin da a ka yi a labarin, amma bai yi bayani ba.

Shekara hudu da su ka wuce, Ms Turay ta kaddamar da sabon bukin al’umman Bondo na farko da ba a yi wa mata kaciya, wand a ke kira Alternative Rites or Bloodless Bondo.

Ta na da yakinin cewa Bondo da kan ta za ta kare idan har ba a daina yi wa mata kaciya ba.

“Idan mata da ko sauran mutane su ka cigaba da goyon bayan yi wa mata kaciya, zai kai wani matsayi da Bondo da kan ta za ta kare. Zai kai matsayin da Bondo za ta tsaya.”