You are here: HomeAfricaBBC2023 04 03Article 1743098

BBC Hausa of Monday, 3 April 2023

Source: BBC

Shin ko Messi zai ci gaba da taka leda a PSG a badi?

Lionel Messi Lionel Messi

Yarjejeniyar da ke tsakanin Paris St Germain da Lionel Messi za ta kare a karshen kakar bana.

Kenan kwantiraginsa zai kara a PSG, idan kungiyar ta lashe Ligue 1 a karshen kakar nan.

PSG tana matakin farko a kan teburi da maki 66 da tazarar shida tsakaninta da Lens, wadda take ta biyu, bayan kammala karawar mako na 29.

Tun da aka shiga kakar 2023, Messi na taka rawar gani, wanda ya ci kwallo shida a wasa 10, amma ya kasa cin Bayern Munich a Champions League.

Tuni aka fitar da PSG daga Champions League a kakar nan da French Cup, kenan Ligue 1 ne kadai a gabanta da take fatan daukar kawo yanzu.

PSG ta sha fadar cewar a shirye take ta tsawaita zaman kyaftin din Argentina a kungiyar.

Mai shekara 35 shi ne kan gaba a ci wa Barcelona kwallaye mai 672 a karawa 778 da ya yi mata.

Dan kwallon ya bar Camp Nou a 2021, bayan da Barcelona ta fada matsin tattalin arziki, da ya sa dole a sayar da shi a kungiyar.

Messi ya dauki Champions League hudu a Barcelona da La Liga 10 da Ballon d'Or shiga a kungiyar ta Sifaniya.

Messi ya amince da kunshin yarjejeniyar kaka biyu da rage masa alabashi, amma hakan bai hana shi barin kungiyar da ya fara tun yana yaro ba.

Wasu rahotanni na cewar Barcelona ta tattauna da PSG kan batun Messi ya sake komawa Camp Nou da murza leda a badi.

To sai dai batun da ake na binciken Barcelona kan kudin da ta biya tsohon mataimakin kwamitin alkalan Sifaya ka iya hana shi kowawa can kada ya fada ruduni.

Ana binciken Barcelona a Sifaniya da Uefa kan biyan kudi ga rafli, domin samun sakamakon wasa da zai amfani kungiyar.

Batun da Barcelona ta musanat aikata ba daidai ba.

Messi wanda ya lashe kofin duniya a Qatar a 2022, ya ci kwallo sama da 100 a Argentina ya haura sama da 800 da ya ci a tarihinsa na taka leda.