You are here: HomeAfricaBBC2023 03 30Article 1740722

BBC Hausa of Thursday, 30 March 2023

Source: BBC

Raphinha ya yi wa Barca dukkan wasa 20 tun bayan Qatar

Raphinha shi ne dan wasa daya tilo da ya buga dukkan wasanni 20 a Barcelona tun wasannin Qatar Raphinha shi ne dan wasa daya tilo da ya buga dukkan wasanni 20 a Barcelona tun wasannin Qatar

Barcelona za ta ziyarci Elche ranar Asabar, domin buga karawar mako na 27 a gasar La Liga.

Kungiyar Camp Nou ta yi wasa 20 a dukkan karawa tu bayan kammala gasar kofin duniya da aka yi a Qatar a 2022, wanda Argentina ta lashe.

Cikin wasannin Raphinha ne kadai ya buga dukkan fafatawa 20 a Barcelona tun daga bayan wasannin Qatar.

Dan kwallon tawagar Brazil na taka rawar gani da Xavi ke amfani da shi a fafatawar da yake fuskanta a kakar nan.

To sai dai Raphinha ba zai yi wasa da Elche ba, sakamakon katin gargadi biyar da ya karba, zai yi hutun karawa daya kenan.

Kawo yanzu a kakar nan, wasa biyu ne dan kwallon Brazil, bai yi wa Barcelona ba, sune tun kafin fara gasar kofin duniya.

Bai yi wasan farko a Champions League ba a fafatawa da Viktoria Pilsen a bana da kuma na La Liga da Athletic Club a Camp Nou.

Kafin fara wasannin kofin duniya an yi fafatawa 20 - kawo yanzu Raphinha ya ci kwallo tara a kakar nan ya kuma bayar da tara aka zura a raga.

Dan kwallon na kara samun kwarewa kan taka leda, wanda ya yi wa Brazil wasanni a Qatar.

Raphinha, wanda ya koma Barca daga Leeds ya ci kwallaye masu mahimmaci a kungiyar Sifaniya a bana, ciki har da wadda ya zura a ragar Osasuna da Valencia da Athletic Club a La Liga.

Barcelona tana matakin farko a teburin La Liga da maki 68, sai Real Madrid ta biyu mai maki 56.