You are here: HomeAfricaBBC2023 03 10Article 1728632

BBC Hausa of Friday, 10 March 2023

Source: BBC

Yadda ƴan Bako Haram suka kashe masunta 30 a jihar Borno

Mayakan Boko Haram Mayakan Boko Haram

Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da kisan fararen hula akalla 30 da mayakan Boko Haram masu kiran kansu ƴan ƙungiyar IS a yankin Afirka ta yamma wato ISWAP a jihar Borno.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Laraba 8 ga watan Maris, a yankin ƙaramar hukumar Gamborun Ngala lokacin mutanen da galibi manoma ne da masunta suka fita neman abin da za su ci.

An kai harin ne kusa da garin Mukdolo wanda ke kusa da wata matattarar ƴan Boko Haram inda mutanen suka shiga don kamun kifi da kuma neman itacen wuta.

Bayan mutanen kusan talatin da maharan suka harbe akwai waɗanda suka tsira amma da raunukan bindiga da kuma wasu da rahotanni suka ce ba a san inda suke ba har yanzu.

Majiyoyin tsaro sun ce gomman mayakan na Boko Haram masu mubayi’a ga ISWAP ne a kan babura suka afka wa dajin da mutanen suka shiga kana suka bude musu wuta da harbin kan mai-uwa-da-wabi.

An ce mutane tara sun yi nasarar tserewa, amma da raunin bindiga.

Wasu bayanai sun ce harin ya biyo bayan gargadin da ‘yan ta’adda suka yi wa mutanen yankin ne kan su kiyayi ratsawa ta wuraren da suka yi tunga.

Wani daga cikin wadanda suka halarci jana’izar mutanen da aka kashe a garin Dikwa, Malam Tijjani M Tahir ya yi wa BBC ƙarin bayani, inda ya ce mutanen da abin ya shafa su sama da talatin ne kuma dukkanninsu ƴan garin ne.

Ya ce a jiya Alhamis ne suka yi jana’izar mamatan wadda har ɗan majalisar dokokin jihar Borno mai wakiltar mazaɓar ya halarta.

Mallam Tijjani ya ce lamarin ya yi matuƙar tayar wa al’ummar garin da ma yankin baki ɗaya hankali.

A cikin wata sanarwa, babban jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da ayukkan jinƙai a Najeriya Mista Matthias Schmale ya yi ta’aziyya da jaje ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa su.

Mista Schmale ya ce harin mai matukar tayar da hankali wata manuniya ce ga cewa ga irin barazana da tashin hankalin da ‘yan gudun hijira da sauran mutanen da ke yankin ke rayuwa a cikin tsawon shekara 13.

Ita ma gwamnatin jihar Borno da kuma masarautar Dikwa sun yi tir da harin tare da yin ta’aziyya ga iyalan waɗanda lamarin ya faru a kansu.

Kakakin gwamnan jihar Babagana Umara Zulum, Isa Gusau ya ce gwamnatin jihar ta kadu da samun labarin wannan harin.

‘’Abin ya baƙanta masa rai matuƙa saboda idan za ka lura cewa mun kwana biyu ba mu samu irin wannan labarin ba.’’

Ya ce, ‘’nan take dai sun kashe mutum 28, mutum shida suka ji ciwo aka kawo suma daga ciki mutum biyu suma Allah Ya yi musu cikawa, yanzu huɗu suna asibitoci a Maiduguri.’’

Kakakin ya ce daman da daɗewa sojoji suna gargaɗin mutane kan su daina zuwa wajen gari, to amma ya ce ba ta yadda za ka ga laifin mutumin da ba shi da abin da zai ci fita.

‘’Saboda na farko dai ya kamata a ce an samar da tsaro ko’ina bai kamata a ce kana cikin ƙasarka a ce akwai inda ba za ka iya zuwa ba,’’ in ji shi.

Sai dai babban jami’in bayar da agajin na MDD ya yi kira ga hukumomin jihar ta Borno da su hanzarta bincike kan wannan ta’asar kuma su hukunta wadanda suka tafka ta.

Ya tunatar da duka bangarorin da ke wannan fadan bukatar su bi dokokin kare hakkin dan adam na kasa da kasa domin kare fararen hula daga a cutar da su.

Majalisar Dinkin Duniyar dai ta kiyasta cewa tashin hankalin na Boko Haram ya yi sanadin mutuwar akalla mutum dubu 350 kawo yanzu tare da raba miliyoyi da garuruwansu daga shekara ta 2009 lokacin da ya fara.