You are here: HomeAfricaBBC2023 03 09Article 1728026

BBC Hausa of Thursday, 9 March 2023

Source: BBC

Kiristocin Iraqi na adawa da haramcin sayar da barasa

Hoton alama Hoton alama

Ƴan siyasa Kirista a Iraqi na ƙoƙarin soke dokar da ta haramta shigarwa da kuma sayar da barasa a ƙasar.

An bai wa jami'an hukumar shige da fice umarni ranar Asabar na su tabbatar da haramcin.

Ya zama doka a watan da ya gabata duk da hamayyar da ake nunawa.

Ƙungiyar, wadda ke da kujeru biyar a majalisar dokokin Iraqi ta shigar da ƙara inda ta ce matakin ba ya bisa doron dumukuraɗiyya.

An haramta shan barasa a bainar jama'a a Iraqi, ƙasar da mafi yawan al'ummarta Musulmai ne.

Amma ana iya sayenta a shagunan sayar da barasa ko kuma shagunan da suka samu lasisin sayar da ita.

Dokar, wadda tun asali majalisar dokoki ta amince da ita a 2016 - kuma ta zama a hukumance, a watan da ya gabata ne wato shekaru bakwai tun bayan da aka amince da ita ta fara aiki.

A ƙarar da suka ɗaukaka, mambobin ƙungiyar Babylon ta dage cewa dokar ta saɓa da kundin tsarin mulki saboda ba ta yi la'akari da ƴancin tsiraru ba.

Dokar ta kuma yi hannun riga da wata doka da aka amince da ita ƙasa da mako guda da ya gabata kafin buga jaridar ƙasar ta The Gazette ranar 20 ga watan Fabarairu inda aka ƙayyade kuɗin fito kashi 200 kan dukkan barasar da aka shiga da ita ƙasar nan da shekaru huɗu masu zuwa, in ji su.

Sarmad Abbas, wani mai harkar sayar da gidaje wanda mazaunin Baghdad ne, babban birnin Iraqi ya shaida wa AFP cewa haramcin zai sa a koma sayar da barasa a kasuwar bayan fage.

Ya ce addinin Musulunci ya haramta shan barasa "amma wannan ƴanci ne da ba za ka iya haramta wa masu sha ba," in ji shi.

A cewar rahotanni, ƙudirin tun farko Mahmoud al-Hassan ne, alƙali a lokacin kuma ɗan majalisa na gamayya ta masu harkokin shari'a ya kawo shi.

Ya ce an yi dokar ne bisa sashe na 2 na kundin tsarin mulkin Iraqi na 2005 wanda ya haramta duk wata doka da ta saɓa wa Musulunci, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.