You are here: HomeAfricaBBC2022 12 07Article 1676378

BBC Hausa of Wednesday, 7 December 2022

Source: BBC

Wane ne Goncalo Ramos? Matashin da ya maye gurbin Cristiano Ronaldo

Goncalo Ramos Goncalo Ramos

Kafin a soma wasan Portugal da Switzerland a gasar cin kofin duniya da Qatar ke daukar bakunci, maganar da ake yi ita ce ta an ajiye Cristiano Ronaldo a benci, amma kuma da aka tashi wasan maganar Goncalo Ramos kowa yake yi.

Matashin, mai shekaru 21, shi ne ya ci kwallo uku shi kadai a wasan da Portugal ta lallasa Switzerland da ci shida da daya.

Ramos ya zama dan kwallo mafi karancin shekaru da ya ci kwallo uku a wasa daya a gasar cin kofin duniya tun bayan dan kwallon Hungary Florian Albert da ya hakan a shekara ta 1962.

Abin da ya kamata ku sani game da Ramos a gasar cin Kofin Duniya

Ramos ya soma wasa ne a cikin tawagar kungiyar Benfica ta matasa kuma sau uku kacal ya tabar buga wa Portugal kwallo kafin wasan da aka buga ranar Talata.

Yana cikin tawagar da ta doke Najeriya a wasan sada zumunci inda ya ci wa Portugal kwallo daya.

A zagayen farko na gasar cin kofin duniya, minti 10 kacal ya buga wasanni biyu tsakanin kasarsa da Ghana da kuma Uruguay.

Ramos ya ci kwallo 14 a cikin wasa 21 da ya buga wa Benfica a kakar wasa ta bana a gasar kwallon Portugal.

Wannan ne karon farko da ya buga gasar cin kofin duniya.

Shi ne dan kwallo na farko da ya ci kwallo uku a wasa daya a gasar cin kofin duniya a karonsa na farko na shiga gasar tun bayan Miroslav Klose na Jamus.

A yanzu an zura ido a ga yadda dan kwallon zai haskaka a wasan Portugal da Morocco a zagaye gab da na kusa da karshe.