You are here: HomeAfricaBBC2022 12 07Article 1676357

BBC Hausa of Wednesday, 7 December 2022

Source: BBC

Masana na tsokaci kan batun Buhari cewa da wuya a yi magudi a zaben 2023 na Najeriya

Hoton alama Hoton alama

Masana siyasa a Najeriya sun fara tsokaci a kan ikirarin da shugaban kasar ya yi cewa da wuya a yi maguɗi a babban zaɓen da ke tafe, sakamakon sauye-sauyen da aka yi na amfani da na’ura a tsarin zaɓen ƙasar.

Sai dai wasu masana na ganin cewa masu maguɗi a ko da yaushe neman sabbin hanyoyi suke yi don cimma burinsu.

Masana siyasa da dama dai  ba su yi mamakin furucin da Shugaba Buharin ya yi game da babban zaɓe mai zuwan ba - na cewa abu ne mawuyaci a yi magudi - bisa la’akari da irin shirin da hukumar zaben kasar ta yi na amfani da na’urorin zamani a lokacin zaɓen.

Mallam Kabiru Sa’id Sufi masanin siyasa ne a kwalejin share fagen shiga jami’a ta jihar Kano, ya ce na’urar tantance masu kaɗa ƙuri’a da aka fi sani da BVAS babu shakka za ta hana magudin zaɓe na al’ada irin na zahiri.

“Gaskiya ne a baya-bayan nan ana samun irin wannan bugar ƙirji da kuma shan alwashi daga shugaban ƙasa da ma shugaban hukumar zaɓe na ƙasa.

“Wataƙila hakan na da nasaba da tanade-tanaden da aka ga an yi na tsare-tsaren zaɓen 2023, ɗaya daga cikinsu shi ne amfani da na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS.

“Ana ganin na’urar ba za ta bayar da damar a yi maguɗi ba kamar yadda ake tunani ko kamar yadda aka yi a baya,” a cewar Mallam Sufi.

Masanin ya ƙara da cewa “sannan kuma ana ganin akwai damar da za a samu ta aikawa da sakamakon zaɓen watakila ta hanyar sadarwa kafin rubutaccen sakamakon ya je ga hukumomi.

“Don haka ana ganin hakan ma zai iya rage ƙarfin son yin maguɗin.”

Sai dai masanin ya ce da maguɗin zaɓe ya taƙaita ga wanda aka sani na zahiri ne - da gaba-gaɗi za a iya bugun-ƙirji a ce BVAS za ta magance shi.

Amma kamar yadda Mallam Kabiru Sufi ke cewa ba a nan take ba, wai an  danne bodari a ka, in ji ƴan magana! Saboda akwai wani magudin na baɗini.

“Harkar magudin zaɓe wani lokacin a kan yi rashin dacewa ya zama kamar ana shan maganin ƙaba kai yana sake kumbura ne.

“Saboda a lokacin da ake ƙoƙarin magance matsalar, sai a ga su masu yin maguɗin suna shirya yadda za su kaucewa tanade-tanaden da za su hana su yin maguɗin zaɓe

Malamin ya ƙara da cewa idan masu maguɗin suka ga an toshe wata damar, “to akwai kuma wani abu da ya kamata a yi tunani don gano yadda za a kauce masa.

“Misali amfani da kuɗi wajen saye ƙuri’un al’umma don sauya musu ra’ayi ko kuma a ba su kudi a karbe katunan zaben nasu don hana su damar kaɗa ƙuri’a.

“Musamman idan da ɗan takarar da aka ga yana da karfi a wajen kuma ake son kayar da shi ta kowane hali,” ya ce.

A ranar Talata ne shugaban Najeriyar ya yi ikirarin cewa zai wuya a yi maguɗi a babban zaɓen ƙasar mai zuwa, saboda kyakkyawan tanadin da hukumar zaɓen ta yi, na amfani da na’ura.

Ya yi wannan bayanin ne lokacin da wani ayarin majalisar dattawan ƙasashen Afirka ta yamma, ƙarƙashin jagorancin shugaban kasar Saliyo, Dr Bai Koroma suka kai masa ziyara a fadarsa da ke Abuja, don jin inda Najeriyar ta kwana a shirin da take yi na babban zaɓe.

Har ma ya yi misali da zaben gwamnan da aka yi a jihohin Anambara da Ekiti da kuma Osun - yana cewa an yi kyakkyawan tsarin da ya bai wa ƴan kasa zaben mutanen da suka kwanta musu a rai ba tare da wata tirsasawa ba!