You are here: HomeAfricaBBC2022 11 06Article 1657601

BBC Hausa of Sunday, 6 November 2022

Source: BBC

Yadda hare-haren ‘yan bindiga ya mayar da garuruwa fiye da 50 kufai a Zamfara

Hoton alama Hoton alama

Har yanzu matsalar tsaro na ci gaba da tabarbarewa a garuruwa da dama na yankunan kananan hukumomin Gumi da Bukkuyum na Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya. Yanzu haka fiye da garuruwa 50 na neman zama kufai a yankunan kananan hukumomin sakamakon yadda hare-haren 'yan bindiga suka tilasta wa jama'ar garuruwan yin gudun hijira zuwa wasu sassan jihar da makwaftan jihohi. Hakan kuma na aukuwa ne duk da kudaden haraji fiye da naira miliyan dari da 'yan bindigan suka karba daga hannun mutanen garuruwan, bisa yarjejeniyar 'yan bindigan za su bari a gudanar da ayyukan noma, a kuma girbe kayan amfanin gona. Mannir Sani Fura Girke, dan jarida nem ai binciken kwakwaf kan harkokin tsaro, ya shaida wa BBC cewa, na yi yarjejeniya da ‘yan bindigar da kuma garuruwa 55, inda suka yar da cewa ba zasu kara kai hare-hare ba muddin aka biya su kudin haraji. Ya ce,” Dukkan garuruwa 55 din sai da suka biya kudinsu wasu miliyan uku wasu miliyan hudu haka aka tara aka basu naira miliyan 172 da dubu dari biyar.” Dan jaridar ya ce ana ga kamar abin ya yi sauki za a samu damar aikin gona, sai yanzu suka sake dawo wa suna kai hare-hare. “ Wadannan hare-hare sun sanya wadannan garuruwa cikin halin ha’ula i, saboda gaba dayan mutanen da ke zaune a garuruwan da ma kauyukansu duk sun yi gudun hijira.” Mannir Sani Fura Girke, ya ce yawancin kayan amfanin gonar da suka yi suke bukatar a kwashe su duk sun zube a kasa, sannan kuma tun da ‘yan bindigar suka lura cewa mutane sun bar garuruwansu sai suka koma cinnawa kayan amfanin gonar wuta. Dangane da batun jami’na tsaro kuwa, dan jaridar ya ce a gaskiya duk wadannan garuruwan ba bu jami’na tsaro sai dai a kananan hukumomi suke. Tuni dai rundunar ‘yan sandan jihar ta ce jami’ansu da ma sauran  jami’na tsaro na sane da irin matsalar tsaron da ake fuskanta a garuruwan kananan hukumomin na Gumi da Bukkuyum. SP Muhammad Shehu, shi nem ai magana da yawun rundunar ‘yan sandan a Zamfarar, ya shaida wa BBC cewa, hadin gwiwar jami’na tsaro na nan na daukar matakan da suka dace a wadanann yankunan don magance matsalar.