BBC Hausa of Tuesday, 25 October 2022

Source: BBC

An kori koci biyu a Premier League a cikin watan Oktoba

Steven Gerrard (tsakiya) Steven Gerrard (tsakiya)

Ranar Alhamis, Aston Villa ta kori Steven Gerrard daga jan ragamar kungiyar, bayan da Fulham ta doke ta 3-0 a wasan mako na 12 a gasar Premier League. Gerrard ya bar kungiyar tana ta 17 a kasan teburi da maki tara, bayan buga wasa 11 a kakar nan. Aston Villa ta ci wasa biyu da canjaras uku aka doke ta karawa shida, ta kuma ci kwallo bakwai aka zura mata 16 a raga a bana. Tsohon dan wasan Liverpool an nada shi kociyan Aston Villa ranar 11 ga watan Nuwambar 2021, wanda ya maye gurbin Dean Smith. Kawo yanzu Gerrard ya ja ragamar Villa wasa 38 da cin 12 da canjaras takwas aka doke shi fafatawa 18. Haka kuma kungiyar ta Villa Park ta ci kwallo 45 aka zura mata 50 a raga karkashin jagorancin Gerrard. Ranar Lahadi 23 ga watan Oktoba, Aston Villa za ta karbi bakuncin Brentford a ci gaba da wasannin Premier League. Wani kociyan da aka sallama a cikin watan Oktoba a Premier League shi ne Bruno Large daga Wolverhampton. Kociyoyin da ke jan ragamar kungiyoyin Premier League 2022/23 Kungiya . Kociya Ranar dauka Wanda ya gada      Arsenal    Mikel Arteta    20 Dec 2019    Unai EmeryBrentford Thomas Frank 16 Oct 2018     Dean SmithBrighton Roberto de Zerbi     18 Sept 2022   Graham PotterChelsea    Graham Potter         8 Sep 2022       Thomas TuchelCrystal Palace  Patrick Vieira   4 July 2021       Roy HodgsonEverton    Frank Lampard         31 Jan 2022     Rafael BenitezFulham     Marco Silva      1 July 2021       Scott ParkerLeeds United   Jesse Marsch   28 Feb 2022     Marcelo BielsaLeicester City   Brendan Rodgers     26 Feb 2019     Claude PuelLiverpool Jurgen Klopp    8 Oct 2015       Brendan RodgersMan City      Pep Guardiola 1 Jul 2016         Manuel PellegriniMan United Erik ten Hag     21 April 2022   Ralf Rangnick Newcastle     Eddie Howe     8 Nov 2021      Steve BruceNottingham Forest  Steve Cooper   21 Sep 2021     Chris HughtonSouthampton  Ralph Hasenhuttl     5 Dec 2018       Mark HughesTottenham         Antonio Conte 2 Nov 2021      Nuno Espirito West Ham United    David Moyes   30 Dec 2019    Manuel Pellegrini Kungiyoyin da ba su da koci kawo yanzu Aston Villa        Wadda ta sallami Steven Gerrard Bournemouth  Wadda ta raba gari da Scott Parker Wolverhampton Bwadda ta kori runo Lage