You are here: HomeAfricaBBC2022 10 24Article 1649318

BBC Hausa of Monday, 24 October 2022

Source: BBC

Gargadin Amurka da Birtraniya da DSS kan yiwuwar hare-hare a Najeriya

Tutar Najeriya Tutar Najeriya

Hankulan mazauna babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, sun tashi bayan sanarwar da Amurka ta fitar tana gargaɗi kan yiwuwar kai hare-haren ta'addanci a Najeriya. A ranar Lahadi da yammaci ne Ofishin Kakadancin Amurka da ke Abuja ya fitar da sanarwar hakan, inda ya ce babban birnin Najeriya ya fi fuskantar barazanar hare-haren ta'adancin. "Wuraren da ke fuskantar barazanar kai hare-haren sun haɗa da wuraren ibada da kasuwanni da makarantu da gine-ginen gwamnati da rukunin shaguna. "Da otel-otel da kantunan cin abinci da mashayu da hukumomin ƙasashen duniya da tasoshin motoci da wuraren wasanni da kuma cibiyoyin tsaro," in ji sanarwar. Ofishin Jakadancin Amurkan ya kuma ce zai rage yawan ayyukansa har sai baba ta gani. Jim kaɗan bayan fitar da saƙon sai shi ma Ofishin Jakadancin Birtaniya da ke Abuja ya fitar da tasa sanarwar kan hakan, yana cewa ba zai buɗe ba a ranar Litinin 24 ga watan Oktoban 2022. "A ranar Litinin 24 ga Oktoba, Ofishin Jakadancin Birtaniya da ke Abuja zai buɗe ne kawai ga ma'aikatan da aikinsu ya zama dole. "Dukkan abokan aiki da ke son zuwa ofishin jakadancin dole su nemi izini daga shugabanninsu kafin yin hakan." Kazalika ofishin ya bai wa ma'aikatansa shawara da kar su kai ƴaƴansu makaranta. "Za mu fitar da ƙrin bayani nan ba da jimawa ba," a cewar sanarwar Birtaniyan. Me Najeriya ta ce? A nata martanin, hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS ta ce ta samu saƙonnin neman ƙarin bayani daga jama'a tun bayan fitar da sanarwar Amurkan a ranar Lahadi. "Idan za a iya tunawa dama hukumar DSS ta sha fitar da irin wannan sanarwa ta gargaɗi kan barazanar kai hare-hare a baya," kamar yadda ta faɗa a wata sanarwa da ta fitar jim kaɗan bayan ta Amurkan. DSS ta shawarci mutane da su ɗauki dukkan matakan kariya da suka dace. "Muna so mutane su zama cikin shirin ko ta kwana tare da taimakon hukumomin tsaro da bayanan da suka kamata na duk wani motsi da ba su yarda da shi ba. Sannan DSS ta nemi mutane da su kwantar da hankulansu a yayin da hukumar ke aiki da sauran hukumomin tsaro da duk masu ruwa da tsaki na ƙasar don tabbatar da doka da oda da zaman lafiya a ABuja da ma sauran sassan ƙasar. Me ya kamata a yi? Ofishin Jakadancin Amurkan a Najeriya a cikin sanarwar tasa ya bayyana wasu matakai ko shawarwari biyar da ya ce mutane su bi don kauce wa duk wani mummunan abu da ka iya faruwa: A guji yin tafiye-tafiyen da ba su zama tilas ba A kasance cikin shirin ko ta kwana A guji shiga cikin cunkoso ko taruka Kowa ya sake duba matakan tsaronsa na ƙashin kai kuma wayoyinku su kasance cike da caji ko yaushe saboda wani abu na gaggawa da ka iya tasowa Ku dinga ɗaukar katin shaidarku duk inda za ku.