You are here: HomeAfricaBBC2022 10 12Article 1640870

BBC Hausa of Wednesday, 12 October 2022

Source: BBC

Sabuwar manhajar karatu na tayar da kura a Kenya

Hoton alama Hoton alama

Wani bidiyo da ke jan hankula a shafukan sada zumunta wanda ke nuna wasu 'yan makarantar firamare aji na biyu na datse kan wata kaza ya tayar da hankula kan sabuwar manhajar karatu ta kasar Kenya. Sabuwar manhajar na son dalibai su fi mayar da hankulansu kan ainihin aiwatar da abubuwan da ake koyar da su maimakon tsabar karatu kawai. Yayin da ake gabatar wa dalibai masu shekaru 11 wani darasi kan yadda ake kashe kaza da kuma dafa ta, an ga wani yaro na danne wata kaza yayin da wani dalibin ke rike da wuka a daidai wuyan kazar. Wasu daliban da ke kallon yadda lamarin ke wakana sun ga lokacin da malaminsu - wanda ke nadar bidiyon lamarin da wayarsa ta hannu - ya yaba wa yaron da ya yanke kan kazar sannan ya umarci yaron da ke rike da jikin kazar ya jefa ta cikin wata tukunyar ruwan zafi. Sai dai yayin da yaron ya saki kazar a daidai bakin tukunyar, sai kazar ta kwace daga hannunsa tana faka-faka da fuka-fukanta kuma ta tsere. Bidiyon, mai tsawon dakika 19, ya kare da dariyar da malamain ke yi yayin da dalibansa suka watse saboda yadda kazar ke zagaye babu kai a tsakaninsu. Wannan bidiyon ya ja hankulan jama'a, inda yawancinsu ke bayyana damuwarsu ga kiyaye lafiyar yaran. Tun da suka fara karatu a makarantar firamare daliban sun kasance abin gwaji kan sabuwar manhajar karatu ta kasar. Masu goyon bayan wannan tsarin na cewa zai taimaka wajen shirya daliban su fahimci inda duniya ta fuskanta maimakon yadda tsohon tsarin ya rika cika musu kai da bayanai. Suna kuma cewa tsarin zai rage satar amsa wada ya zama gagarumar matsala ga gwamnatin Kenya. Kimanin dalibai miliyan 1.25 ne ake sa ran za su rubuta jarabawar kammala karatun firamare, wadda za ta ba su damar shiga makarantun sakandaren kasar. A karon farko za a ba jarabawar maki 40 cikin 100, inda sauran makin zai fito ne daga ayyukan kai tsaye da za a rika yi musu. 'Cin dadi da kudin iyaye' Sai dai wasu iyayen ba su ji dadin yadda sauyin ya shafi 'ya'yan nasu ba. Babban dalili shi ne yadda ake matsa musu su tara kudi domin sayen kayayyaki kamar kajin da ake amfani da su. Wani malamin kimiyya a makarantar firamare ta Kangundo a gabashin Kenya ya ce yaran da suka fito daga gidajen marasa galihu sai dai su kalli sauran 'yan uwansu na gudanar da darussa. Amma malama Marion Muthoni mai koyarwa a birnin Nairobi ta ce darussan da ake koyar da daliban na ba malamai zabi biyu ne: dalibai na iya koyon ninkaya ko su koyi yadda ake tsalle da igiya. Ta ce, "Wasu malamai na zuzuta al'amarin. Abubuwan da nake gani a shafukan sada zumunta ba su yi daidai da tsarin karatu da aka ba mu ba. Sannu a hankali malamai za su fahimci cewa ba komai ne ya dace a ce sai an koyar da dalibai kai tsaye ba." Tana ganin kuma wasu malaman na amfana da tsarin - inda suke bukatar dalibai su kai musu nama, amma ta ce babu nama cikin darasin yadda ake yin miya. "Makarantar da nake aiki na wani kauye ne da iyalai ma da kyar suke iya sayen abin da za su ci saboda haka ne ba zan taba bukatar dalibaina su kawo min nama ba." Bayan bidiyon darasin yanka kaza ya karade shafukan sada zumuntar kasar, sai aka ga wani bidiyon na daban wanda ke nuna wasu malamai na cin naman kaza a cikin ofishinsu. Wani dan majalisa daga yammacin kasar ta Kenya ya zargi malaman da lakume abincin da iyaye suka tara kudin da kusan ya fi karfinsu. Rikicin ya kai ga kunnuwan sabon shugaban kasar William Ruto, wanda tuni ya nada wani kwamitin mutum 49 domin ya sake duba manhajar karatun. Ya bai wa kwamitin zuwa karshen wannan shekarar ya mika rahotonsa. Shawarar da kungiyar malamai ta Kenya KNUT ta bayar bayan da aka kammala gwajin sabuwar manhajar na shekara biyu ita ce a jinkirta fara aiki da ita har zuwa lokacin da aka ba malaman kasar horarwa sosai. Wasu iyayen da ba za su iya biyan kudaden da ake karba a hannunsu akai-akai ba sun gwammace mayar da 'ya'yansu makarantu as zaman kansu. Wasu malaman kuma na ganin gwmnati ce ya kamata ta rika ba makarantu tallafi kayayyakin gudanar da darussa, sai dai ko za ta hada da kaji wani abu ne na daban.