You are here: HomeAfricaBBC2021 06 07Article 1280524

BBC Hausa of Monday, 7 June 2021

Source: BBC

Yarima Harry da maiɗakinsa Meghan sun sami karuwar jaririya

Yarima Harry da maiɗakinsa Duchess Meghan Yarima Harry da maiɗakinsa Duchess Meghan

Duke na Sussex Yarima Harry da maiɗakinsa Duchess Meghan sun sanar da cewa sun sami ƙaruwar jaririya.

An haifi Lilibet "Lili" Diana Mountbatten-Windsor ne da safiyar ranar Juma'a a wani asibiti da ke birnin Santa Barbara ta Jihar California.

Wata sanarwa da iyalan gidan Yarima Harry su ka fitar na cewa jaririya Lilibet da mahaifiyarta Meghan na cikin koshin lafiya a gida.

Fadar Buckingham ta ce: "Sarauniya da Yariman Wales da Duchess na Cornwall da kuma Duke da Duchess na Cambridge na murnar samun wannan labari mai faranta rai."

Yarima Harry da Meghan sun sanar da cewa sun raɗawa jaririyar, wadda ita ce ta biyu cikin 'ya'yansu, sunan Lilibet saboda wani laƙani ne da ake kiran Sarauniya da shi, wadda ita ce mahaifiyar kakan jaririyar.

Ɗaya sunan na ta wato Diana, sun zaɓo shi ne domin karrama kakarta marigayiya Gimbiya Diana ta Wales, inji sanarwar.

  • Meghan da Harry sun ziyarci masallaci mai tsohon tarihi
  • Hotunan auren Yarima Harry da Meghan Markle
An dai haifi Lilibet ne da karfe 11:40 agogon Jihar California ta Amurka, kuma a halin yanzu tana gida tare da iyayenta.

Ita ce tattaɓa-kunnen Sarauniya ta 11, kuma ta takwas a jerin wadanda za su gaji gadon sarautar Ingila.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya aika da sakon taya murnarsa ga iyayen, kuma jagoran jam'iyyar adawa ta Labour Sir Keir Starmer ma ya yaba da labarin da ya samu na haihuwar.

Yarima Harry mai shekara 36 ya fara ganin Meghan ce mai shekara 39 yayin wani biki da aka yi a fadar Windsor, kuma a watan Mayun 2018 su ka yi aure, inda bayan shekara guda kuma su ka sami karuwar da namiji mai suna Archie Harrison Mountbatten-Windsor.

Saboda janyewa da Yarima Harry da mai dakinsa Meghan su ka yi daga ayyuka a fadar Ingila kuma su ka koma Amurka da zama, jaririya Lilibet ta kasance jikar gidan ta farko da aka taba haihuwa a wata kasar waje.


Why Lilibet?

Lilibet - wanda laƙanin Sarauniya ne - ya zama inkiyarta ne tun ta na ƙarama kuma ba ta iya faɗin sunanta "Elizabeth" sosai.


A watan Nuwamba, Meghan ta bayyana cewa ta yi ɓarin cikin da ta ke ɗauke da shi cikin watannin da su ka gabata. Ta bayyana cewa ta shiga wani mawuyacin hali cikin wani labari da ta wallafa da kanta a jaridar New York Times.