You are here: HomeAfricaBBC2021 06 07Article 1280419

BBC Hausa of Monday, 7 June 2021

Source: BBC

Za a fara aikin cire itatuwa da duwatsu a kogin Kwara

Hoton masu ceto muntane a wani hatsarin jirgin ruwa Hoton masu ceto muntane a wani hatsarin jirgin ruwa

Hukumar Kula da raya kogunan da ke samar da wutar lantarki a Najeriya ta ce a yau Lahadi ne za ta aikin safiyo kan kogin Kwara domin sare itatuwa da kuma cire duwatsu da ke kasansa a kokarin magance afkuwar hadurran jiragen ruwa a kogin.

Shugaban hukumar Abubakar Sadiq Yelwa, ya shaidawa BBC cewa makasudin yin wannan aikin shi ne magance matsalar da ake fuskanta na yawan hadarin da jiragen ruwa suke yi a Najeriya a baya-bayan nan.

Makasudin samar da hukumar shi ne samawa al'umomin da ke zaune a gabar kogin Kwara saukin halin da suke ciki, musamman na yawan hadarin jiragen ruwan.

Abubakar Yelwa ya ce aikin na hadin gwiwa ne, domin sun tuntubi hukumar kula zirga-zirga a kogi, da masarautar Yawuri, da masarautar Bargu, da sarakunan ruwan wadannan masarautu, da kungiyoyin masu zirga-zirga a kan kogin na Kwara, domin su kai ziyara wuraren da ake da matsalar fitowar itatuwa da duwatsun da ke cikin kogin, sannan a samu yankewa da kwashewa.

Baya ga wannan aikin, hukumar kula da raya kogunan ta bada umarnin sayo allon da ke dauke da alama da za a sanya a duk inda duwatsu suke a cikin kogin, kafin lokacin da za a kwashe su.

Sannan hukumar ta tanadi kayan aikin da ake bukata musamman na yanke bishiyoyin da kuma na kauda duwatsun da ke kasan ruwa.

Yelwa ya ce ''hikimar hakan ita ce, a duk lokacin da matuka jiragen ruwa suka doshi wannan wuri, za su hango alamar da ke nuna akwai duwatsu a wajen ta yadda za su kauce hakan kuma zai taimaka wajen rage yawan hadarin da aka fuskanta na jiragen ruwa a baya-bayan nan.''

''Aikin za a yi shi ta fuska biyu, na farko za a fara daga Bargu zuwa Samanaji, zuwa Malale, da kuma Wara. Sannan kuma za a dauko aikin daga Wara zuwa Zamare da Yawuri har zuwa Gyabe har zuwa Dole Kaina.

Muna sa ran zuwa tsakiyar ko karshen watan Yuli za a kammala aikin sare itatuwan. Domin idan ba a yi wannan aikin ba a wannan lokacin to sai dai a hakura zuwa shekara mai zuwa, saboda a yanzu ne itatuwan suke fitowa domin ruwan kogin na yin kasa.

Amma daga tsakiyar watan Bakwai na shekarar nan ruwan zai sake dawowa, kuma da zarar ya dawo zai rufe itatuwan ba za a gansu kamar yadda ake gani a halin yanzu ba.

Kuma dukkan wadanda lamarin ya shafa kama daga al'umomin yankin da kungiyoyi da masarautu duk sun ba mu hadin kai domin yin wannan aikin,'' inji Yelwa.

Wannan aikin na zuwa ne bayan samun mummunan hadari jirgin ruwan da aka yi a jihar Kebbi a baya-bayan nan, da sama da mutum 100 suka mutu.

Sannan an sake yin wani hadarin jirgin ruwan a jihar Sakkwato mai makoftaka da Kebbin da nan ma mutane da dama suka rasa rayukansu.