You are here: HomeAfricaBBC2021 06 07Article 1280233

BBC Hausa of Monday, 7 June 2021

Source: BBC

Muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a makon nan

Gwanmatin Buhari ta dakatar da shafin Twitter Gwanmatin Buhari ta dakatar da shafin Twitter

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a makon da ya gabata a Najeriya, daga Lahadi 30 ga Mayu zuwa Asabar 5 ga Yuni.

Najeriya ta dakatar da shafin Twitter

Shafin Twitter ya daina aiki a Najeriya bayan da gwamnatin kasar ta dakatar da shafin a ranar Juma'a.

An lura shafin ya daina aiki ne a tsakiyar daren Juma'a wato wayewar garin ranar Asabar.

Mai dakin shugaban Kasar Najeriya Aisha Buhari ta rufe nata shafin domin nuna goyon baya ga matakin da kasar ta dauka na dakatar da shafin.

Wata sanar da ma'aikatar yada labarai da al'adu ta fitar, ta ce Minista Lai Mohammed ne ya ba da sanarwar a Abuja a ranar Juma'a.

Sanarwar ta ce Minista Mohammed ya ce ana amfani da shafin wajen raba kawunan ƴan ƙasar.

Lai Mohammed ya kuma ce ya bai wa hukumar kula da gidajen rediyo da talbijin ta ƙasar NBC ta fara shirye-shiryen ba da lasisi ga kafafen yaɗa labarai na intanet.

Dalilin dakatar da Twitter a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta fusata ne kan sakon shugaba Muhammadu Buhari da kamfanin Twitter ya goge.

A ranar Laraba ne Kamfanin Twitter ya goge ɗaya daga cikin jerin saƙwannin da Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa a ranar Talata.

Twitter ya goge inda shugaban ya ce "matasan yanzu ba su san girman ɓarna da hasarar rayukan da aka yi ba a yaƙin basasa ba. Mu da muka shafe wata 30 a fagen daga, muka ga bala'in yaƙin, za mu bi da su da salon da suka fi ganewa," in ji Buhari.

Daga baya ne kuma Twitter ya goge sakon daga shafin shugaban na Najeriya.

Batun ya ja hankalin gwamnati da ƴan Najeriya matakin da ya kai ga dakatar da Twitter baki ɗaya a ƙasar.

Satar ɗaliban Islamiyya a Neja

A ranar Lahadi ne ƴan bindiga suka makarantar Islamiyyar a garin Tegina a jihar Neja suka saci ɗalibai kusan 150 da malamansu guda uku

Ƴan bindigar sun sace gwamman daliban makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko, koda yake sun saki wasu daga cikin daliban saboda kanana ne amma hukumomin makarantar sun tabbatar wa BBC cewa ɗalibai 136 ne suka kididdige san sace.

A cewar shaidun 'yan bindigar sun rika harbi kan mai-uwa-da-wabi kafin daga bisani su dauke daliban.

Cikin wata sanarwa da gwamantin jihar ta fitar ta ce an harbi mutum biyu lokacin harin kuma an tabbatar da mutuwar daya daga ciki, yayin da guda ke cikin mawuyacin hali.

A ranar Laraba Shugaban makarantar Islamiyyar Salihu Tanko Islamiyya ta ƙaramar hukumar Rafi a jihar Neja, Malam Abubakar Garba Alhassan ya shaida wa BBC cewa Iyaye mata biyu na ɗaliban Islamiyyar sun rasu sakamakon kaduwar da suka yi bayan da suka sami labaran sace 'ya'yansu da 'yan bindiga suka yi,

Makomar 'Mijin Aljana' a Kano

Gwamnatin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta sanya wa mutumin da ya yi ikirarin cewa shi mijin aljana ne takunkumi na sayar da magungunan damfara ga al'umma.

A ranar Litinin ne Kwamishinan harkokin addini na jihar Muhammad Tahar wanda aka fi sani da Baba Impossible ya sanar wa BBC Hausa sun ɗauki mataki akansa bayan kammala taron muƙabala da shi.

A kwanakin baya ne wasu kafafen yaɗa labarai suka ruwaito cewa Malam Ahmad Ali Kofar Na'isa ya yi ikirarin cewa tun yana yaro ya faɗa a rijiya aljanu suka ɗauke shi suka mayar da shi Masar tsawon shekara shida.

Ya kuma ce daga bisani sun mayar da shi wajen mahaifiyarsa, sannan a yanzu yana auren aljana har suna da ƴaƴa uku.

Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce ƙwarai da gaske a tsakanin mutane inda ya zama abin al'ajabi ga wasu yayin da wasu kuma ya ba su taƙaici.

Baba Impossible ya ce cikin sharuɗɗan da aka gindaya wa Mijin Aljana har da hana shi tara mutane mata da maza a gidansa kamar yadda yake yi.

Sannan an hana shi magana da 'yan jarida, tare da rusa rumfar da yake tara mutane.

Gwamnati ta hana shan sigari a bainar jama'a a Kano

A ranar Litinin ne gwamnatin jihar Kano ta haramta shan taba sigari a bainar jama'a don magance annobar shan tabar, yayin da Najeriya ta yi ƙiyasin cewa mutum 16, 100 ne ke mutuwa duk shekara dalilin cutukan da suka danganci shan tabar.

An ruwaito gwamnatin ta jihar Kano na cewa ta ɗauki matakin ne a wani yunƙuri na inganta lafiyar al'ummar jihar .

An ambato Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa kwamishinan lafiya na jihar yana cewa gwamnatin na aiki ba dare ba rana wurin ganin ta rage yawan mutane masu shan taba a jihar.

Ya kuma ce akwai wani ƙudirin doka a halin yanzu a majalisar dokokin jihar da ake fatan za ta samar da hukumar yaki da miyagun ƙwayoyi wadda za a ɗora wa alhakin tabbatar da cewa shan miyagun ƙwayoyi ya ragu a jihar.