You are here: HomeAfricaBBC2021 05 30Article 1274161

BBC Hausa of Sunday, 30 May 2021

Source: BBC

Yadda nau’ukan husufin rana da wata ke aukuwa

Husufin wata da rana na iya aukuwa ne sanadiyyar juyin falakin taurari Husufin wata da rana na iya aukuwa ne sanadiyyar juyin falakin taurari

Husufin wata da rana na iya aukuwa ne sanadiyyar juyin falakin taurari.

Akwai kwakkwaran dalili, da ke nuni da cewa, daukacin nau'ukan kai-kawon turari da wata da rana na aukuwa ne don bayyana ga masu bukatar ganinsu.

Husufin rana da ake sa ran aukuwarsa shi ne na ranar 26 ga Mayu - inda ake sa ran ganin daukacin husufin ranar daga Gabashin Asiya da Austiraliya da daukacin yankin Pacific da nahiyar Amurka.

"Daukacin al'amarin, na nuni da cewa akwai nau'uka biyu na husufin: wato na rana da wata" kamar yadda Juan Carlos Beamín, wani masanin taurarin sararin samaniya ya bayyana a rubutunsa da ala wallafa a Cibiyar nazarin Sadarwar Kimiyya da ke Jami'a mai cin gashin kanta ta Kasar Chile (Autonomous University of Chile,).

Yadda yake kunshe a wani littafinsa mai taken Ilimin sararin samaniya a bayyane (Illustrated Astronomy).

Sai dai ya yi nuni da cewa: A fahimtar qwararrun masana akwai nau'i na uku, wanda ya danganci taurari biyu." A nan za a iya bayyana nau'uka uku da bambance-bambancensu:

HUSUFIN RANA

A wasu lokutan, yayin da Wata ke kewaya falakin Duniya, inda yake a tafiya a tsakanin rana da duniyarmu, ya tare/toshe hasken tauraro, al'amarin da ke haifar da husufin rana.

A wata mahangar, Wata na yi wa sararin duniya inuwa ya lullubeta. Sai dai akwai nau'ukan husufi rana, wadanda suka bambanta da juna ta yadda suke dusashe hasken rana.

Daukacin husufin rana

Daukacin husufin rana yana aukuwa ne yayin da Rana da Duniya da Wata suka yi kai-da-kai (kamar za su hadu a hanya guda mikakkiya), ta yadda watan zai toshe hasken rana dungurungum.

A wasu 'yan dakikoki (a wasu lokuta ko ma mintuna), sama kan yi matukar duhu, inda takan nuna tamkar dare ne.

A cewar Cibibiyar Sararin Samaniyar Amurka ta NASA, "daukacin husufin rana suna faruwa a duniya sanadiyyar karfin al'amuran da ke faruwa a saman duniya:"

Rana ta rubanya Wata fadi sau 400, sannan kuma tana nisan daga gare shi da ninki 400.

"Layukan zayyanar lissafi na tabbatar managarciyar haduwa mikakkiya, inda Wata kan toshe daukacin sashen rana, ta haifar husufin rana dungurungum," yadda NASA ta bayyana.

Layin da ke bin sawun dundumin duhun wata a daukacin fadin duniya shi ake kira"tafarkin dungurungum- ko duhu mai gaba daya" kuma yana kasancewa ne a wani dan karamin sashe da ke nuni da duhu dungurungum da ake iya gani.

A daukacin gefen zirin layin, da ke da nisan dubban kilomita, za a iya ganin dishi-dishin husufin.

Kwatankwacin nisan da aka yi da zirin duhun dungurungum, wani karamin sashen rana Wata zai lullube shi.

Dangane da tsawon lokacin aukuwar al'amura, ya dogara ne kacokam kan"mazaunin duniya da bangaren rana da ke baibaye da duhu," kamar yadda yake a rubutun Beamin.

"A mahangar kiyasi, tsawon husufi rana kan kasance mintuna 7 da dakikoki 32," kamar yadda masanin taurarin sararin samaniya dan kasar Chile ya bayyana.

Dangane da yanayin aukuwar al'amuran, ba wai ba sa kasancewa akai-akai ba, tamkar yadda kake tunani: lamari daya kan kasance a cikin kowane watanni 18.

Abin da kawai ya kasance banbarakwai (na daban) shi ne husufin rana dungurungum, wanda ake iya gani karara a wuri guda, wani lokacin ma yakan kasance cikin akalla kowane shekaru 375.

Za a samu aukuwar husufin rana dungurungum a wannan shekarar ranar 4 ga Disamba, amma akwai bukatar ka kasance a yankin Antartica don ganin tasirin cikakken lamarin.

Husufin hasken gefen rana

Yayin da Wata ya yi nesa da Duniya, sannan ya "kankance" ba ya iya dusashe hasken rana gaba daya.

Saboda haka sai ya yayi wa rana kankanen zobe da ake iya gani karara a kewayen Wata, kuma wannan yanayi ana yi masa lakabi da Husufin hasken gefen rana.

Tamkar yadda ake samun daukacin husufin rana, a lokacin aukuwar lamarin akwai "ketawar haske a gefe da gefen rana " inda ake ganin husufin bai dusashe gefe da gefen rana ba.

A kowane gefen da ya keta, ana iya gani, wani yanki da ke da dishi-dishin husufi.

A ranar 10 ga Yunin 2021, ana sa ran ganin husufin hasken gefen rana a sassan da ke kan layukan latitudes da suka hada da Kanada da Greenland da Rasha, wanda za su ganshi cikakkensa, amma mafi yawan Turai da Tsakiyar Asiya da qasar Sin za su ga husufin dishi-dishi ne.

A ruwayar NASA, wadannan nau'ukan husufin sukan kasance na mafi tsawon lokaci, tunda kawanyar zoben da ake gani kan kwashe tsawon mintuna goma, amma daukacinsu gaba daya ba sa wuce mintuna biyar zuwa shidda.

Gamin-gambizar Husufi

Beamín ya yi nuni da cewa gwamuwar (gamin-gan-bizar) husufi na faruwa ne, "yayin da Wata ked a nisa daga inda zai iya lullube rana gaba daya.

Amma, yayin da yake matsowa, ya kusanto kadan-kadan daga duniya, sai ya dakatar da husufin rana, inda yak an rikide ya zama husufin rana da ke nuna gefenta da haske karara."

Sannan yakan fara a matsayin husufin da ke nuna gefe da gefen rana karara, har daga bisani ya hade ya zama cikakken husufi," a cewar Beamin.

Nau'ukan gamin-gambizar husufi ba su cika aukuwa ba, (sukan kwashi kaso 4 ne cikin 100 na daukacin nau'ukan husufin rana), kamar yadda cibiyar nazarin taurarin samaniya ta IAC ta bayyana.

Bayanan da Cibiyar nazarin sararin samaniyar Amurka ta NASA ya nuna cewa, al'amari na karshe da ya auku, shi ne na shekarar 2003, kuma sai an jira kafin ya sake aukuwa nan da shekara ta 2023, wanda za a iya ganinsa karara a kasashen Indonesiya da Austiraliya da Papua New Guinea.

Daukacin Husufin Wata

A lokacin da aka samu daukacin husufin wata, kamar yadda Cibiyar binciken sararin samaniyar Amurka ta NASA ta bayyana, wata da rana kan kasance a bangarorin duniya daban-daban (sun yi hannun riga da juna).

"Ko da yake Wata hi ne lullube duniya da innuwa - NASA ta tabbatar da cewa hasken rana na kai wa ga wata."

Hasken na ketawa cikin sararin duniya, wanda ke rairaye shi ya fitar da shudin haske.

Wannan shi ne dalilin da ya sanya, a lokacin da lamarin ke aukuwa, mahangar falakin duniya da ke tattara bayanai ke nuna launin ja, wanda ake yi wa lakabi da "Jinin Wata."

A cewar Cibiyar Nazarin Taurarin sararin Samaniya ta Kanada (IAC), "saboda fadin sararin duniya na da nunkin rubi hudu na fadin wata, sai sai lullumin inuwar ya kasance faffada, ta yadda daukacin husufin watan na wanzuwa ne cikin mintuna 104."

Daya daga jerin nau'ukan wannan husufin zai auku ne a ranar 26 ga Mayun 2021.

Idan kana zaune a yankin Kudancin Amurka da Kudu maso gabashin Asiya ko sassan da ke Yammacin Amurka kuma ka yi sa'ar ganin sararin sama wasai za ka kasance ka ga "kyakkyawan furen cikakken wata" daukacin husufinsa da zai shafe kimanin mintuna 14.

Dishi-dishin husufin wata

Tamkar yadda sunan ke nuni, husufi saisa-saisa (kadan-kadan) zai auku yayin da wani yanki na wata yak eta lullumin inuwar Duniya.

Al'amarin dai ya dogara ne a kan kimar husufin, a launin duhun ja ko fatsi-fatsi ko toka-tokar gawayi wanda ka iya bayyana a sashen da watan ya dusashe.

A ruwayar NASA, yayin da daukacin husufin wata ba al'amarin ya cika aukuwa ba ne, mai yanayin kadan-kadan kuwa na aukuwa sau biyu a shekara.

A kan samu husufin wata saisa-saisa a tsakanin ranakun 18 zuwa 19 na Nuwa, wanda ake iya gani a nahiyoyin Arewaci da Kudancin Amurka da Austiraliya da wasu sassan Turai da Asiya.

Husufin dusashewar wani sashen wata

Lamarin na aukuwa ne yayin da wata ya keta ta cikin lullumin dundumin duhun Duniya, wato wannan na nufin ya kara dusashewar duhu.

Saboda haka, irin waxannan nau'ukan husufi na da kyawun gani ta yadda idon mutum ke ganinsu a wani bangaren wata da ya keta ta cikin dundumin duhun watan; kankantarsa na nuni da cewa, yana da matukar wahalar gani.

Saboda wannan dalilin ne, nau'ukan husufin ba cika bayaninsu a lissafin kwanakin shekara na kalanda ba, wata ake fitarwa don kowa da kowa, sabanin masana kimiyya.

NAU'UKAN HUSUFIN TAURARI

Ba daukacin nau'ukan husifi ba ne ake danganta su da Rana da Wata: akwai nau'ukan husufi da ake danganta su da taurari masu nisa.

"Kashi 50 cikin 100 na taurari da ke kewayen falaki, wato biyu ko taurari masu yawa," kamar yadda Beamin ya fada a littafinsa, Ilimin Taurarin sararin samaniya a Bayyanai," wanda ake iya samu a kafar intanet.

"Tun da akwai taurari masu yawa a dandazon taurarinmu, wasu daga jerin taurari rubi biyu alakarsu ta bayyana karara, inda suka hade da Duniya.

Don haka a wani sashe na falaki, wani tauraron na ketawa ta gaban sauran, sannan ya dusashe hasken wanda ke gefensa/bayansa," inji shi.

"Wadannan taurari masu rubi biyu ana yi musu lakabi da taurari masu bangare biyu."