You are here: HomeAfricaBBC2021 05 29Article 1273567

BBC Hausa of Saturday, 29 May 2021

Source: BBC

Me ya sa ake yi wa wasu manyan sojoji ritaya kafin naɗa sabon babban hafsa?

Manjo Janar Farouk Yahaya ne sabon babban hafsan sojin ƙasan Najeriya Manjo Janar Farouk Yahaya ne sabon babban hafsan sojin ƙasan Najeriya

Rahotannin da ke cewa wasu janar-janar na sojoji sun yi ritaya saboda naɗa sabon Babban Hafsan Sojan Ƙasa na Najeriya Farouk Yahaya da Shugaba Buhari ya yi ba sabon abu ba ne a rundunar sojan Najeriya, a cewar masana.

Baya ga hanyar da aka sani ta yin ritaya, akwai kuma tanade-tanaden da ke cikin tsarin aiki na Harmonised Terms and Conditions of Service da kuma dokar aikin soja ta Armed Forces Act of the Nigerian Army, waɗanda suka fayyace yadda za a yi ritayar.

A ranar Alhamis, 27 ga watan Mayu Shugaba Buhari ya naɗa Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin Babban Hafsan Sojan Ƙasa, wanda ya fito daga rukuni na 37 na rundunar sojan Najeriya.

Naɗin nasa ya zo ne 'yan kwanaki bayan rasuwar Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da wasu sojoji 10 a hatsarin jirgin sama da ya faru a filijn jirgin sama na Kaduna yayin da suke kan balaguron aiki.

Kafin naɗin Janar Yahaya, shi ne shugaban runduna ta 1 ta sojojin Najeriya kuma shugaban rundunar Operation Hadin Kai da ke yaƙi da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi a arewa maso gabashin Najeriya.

Babu tabbas game da dalilin da ya sa Buhari ya tsallake sauran manyan janar ɗin ya naɗa Farouk Yahaya.

Sai dai bisa tanadin kundin dokar aiki ta sojoji, naɗin nasa zai tilasta wa wasu sojoji manya yin ritaya da ke rukuni 35 da 36.

'Wannan ba sabon abu ba ne'

"Ba wannan ne karon farko ba da irin haka ke faruwa, daga ranar da duk wani soja ya shiga kwalejin horar da sojoji zai san cewa haka ake yi," a cewar Sani Kukasheka Usman, tsohon kakakin rundunar sojan Najeriya.

Sheka ya ce duk da cewa naɗin zai shafi wasu manyan sojoji, rundunar na da wani tsari wanda ba duka manyan sojojin ne za su yi ritaya ba.

A cewarsa: "Janar Yahaya ya fito ne daga rukuni na 37, janar-janar daga rukuni na 35 da 36 har ma da wasu daga 37 za su iya riƙe wasu muƙaman waɗanda ba lallai ne su kasance a ƙarƙashin shugabancin babban hafsan sojan ƙasa ba.

"Baya ga maganar cewa bai kamata a siyasantar da naɗin shugaban ba, abin tambaya shi ne ko wanda aka naɗa ɗin zai iya aikin da ba shi ko kuma a'a.

"Ina mai tabbatar muku cewa Janar Yahaya na da ƙwarewar da zai iya wannan aikin."

Duk da cewa rundunar ba ta bayyana a hukumance adadin janar ɗin da za su yi rityar ba, rahotanni na cewa kusan 30 ne naɗin nasa zai shafa.

Lokacin da Buhari ya naɗa sabbin hafsoshin tsaro a Janairu, janar-janar kusan 300 ne suka yi ritaya daga ɓangarori daban-daban na sojan ƙasa da na ruwa da na sama 'yan rukuni na 34 da 35.