You are here: HomeAfricaBBC2021 05 19Article 1265542

BBC Hausa of Wednesday, 19 May 2021

Source: BBC

Jamus ta kira Muller da Hummels gasar kofin nahiyar Turai

Kocin Jamus ya sake kira Thomas Muller (hagu) da Mats Hummels Kocin Jamus ya sake kira Thomas Muller (hagu) da Mats Hummels

Tawagar kwallon kafar Jamus ta kira dan wasan Bayern Munich, Thomas Muller da na Borussia Dortmund, Mats Hummels don buga mata gasar cin kofin nahaiyar Turai.

Koci Joachim Low ya gayyaci 'yan wasan cikin 26 da za su buga mata wasannin, duk da cewar a watan Maris din 2019 ya fada musu cewar ba zai gayyace su ba.

Muller, mai shekara 31 ya ci kwallo 11 ya kuma bayar da 18 aka zura a raga da Bayern Munich ta lashe kofin Bundesliga na bana.

Shi kuwa Hummels, mai shekara 32 ya lashe kofin kalubalen Jamus a Dortmund.

A Nuwambar 2020 Jamus ta sha kashi da ci 6-0 a hannun Spaniya a Nations League, karawar da aka zura wa Jamus kwallaye da yawa a tarihin tamaula.

Haka kuma Jamus ta gayyaci matashin dan wasa mai shekara 18, Jamal Musiala cikin tawagar.

Musiala wanda aka haifa a Stuttgard ya zabi buga wa Jamus tamaula maimakon Ingila ko kuma Najeriya.

Jamus tana rukuni na shida a gasar cin kofin nahiyar Turai tare da Faransa da Hungary da kuma Portugal.

Za a buga wasannin tsakanin 11 ga watan Yuni zuwa 11 ga watan Yuli a gasar da ya kamata a fafata a bara, amma cutar korona ta kai tsaiko.

'Yan wasan Jamus:

Masu tsaron raga: Manuel Neuer, Kevin Trapp, Bernd Leno

Masu tsaron baya: Antonio Rudiger, Mats Hummels, Matthias Ginter, Niklas Suele, Emre Can, Lukas Klostermann, Robin Gosens, Robin Koch, Christian Gunter, Marcel Halstenberg

Masu buga tsakiya: Joshua Kimmich, Ilkay Gundogan, Kai Havertz, Toni Kroos, Leon Goretzka, Leroy Sane, Jonas Hofmann, Florian Neuhaus, Jamal Musiala

Masu cin kwallo: Serge Gnabry, Thomas Muller, Timo Werner, Kevin Volland