Cacar baki ta kaure tsakanin Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El-Rufa'i da Kugiyoyin kwadago na Najeriya, sakamakon matakin da gwamnan ya dauka na korar ma'aikata sama da 3,000.
Kungiyoyin kwadago sun sha alwashin tsunduma yajin aiki tare da zanga-zanga daga karfe 12 daren ranar Asabar, saboda korar ma'aikata sama da 3,000 da suka ce gwamnan ya yi.
Akwai kungiyar ma'aikatan jinya da na unguwar zoma, da kungiyar ma'aikatan ilimi da ba malamai ba, da kuma ta ma'aikatan gidajen rediyo da na talabijin da dai sauransu.
Sai dai Gwamnatin El-Rufa'i ta fitar da sanarwa a ranar Asabar dake cewa bai hana tafiya yajin aikin ba, amma dokar kungiyar ta yi bayani karar kan haramtawa ma'aikatan da aikinsu ya zama wajibi shiga yajin aiki.
Gwamnatin Kaduna ta ce ta sanar da jami'an tsaro su dauki mataki kan wadanda suka shirya yajin aikin tare da zanga-zanagar da ake ganin za ta iya rikidewa zuwa tashin hankali.
"Bayan haka akwai maganar dokar annobar korona wadda ta haramta gudanar da manyan taruka a jihar Kaduna.
"Kuma an sanya wannan doka ne saboda dakile irin wadannan tarukan da ko an fara su cikin ruwan sanyi suke rikidewa su koma rikici," in ji sanarwar.
Gwamnatin Kaduna ta ce za ta yi duk mai yiwuwa domin kare dukiyoyi da kuma ma'aikatanta a fadin jihar.
Kuma a cewarta abu ne da ya haramta wani ya hana ma'aikata shiga ofisoshinsu domin gudanar da aiki.
"Ofisoshin gwamnati ba mallakar wata kungiya ba ce da wani zai kulle su ko kuma ya lalata abin da ke cikinsu".
Wannan matakin yajin aiki za a dauke shi ne na tsawon kwanaki biyar a fadin jihar domin bin hakkin ma'aikata a cewar gamayyar.
Me zai faru idan El-Rufa'i ya ki sauraronsu?
Cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC shugaban Kungiyar kwadago ta kasa Kwamared Ayuba Waba ya ce, idan aka kwashe kwanaki biyar da aka diba gwamnati bata neme su ba to yajin aikin zai koma na kasa baki daya.
Ayuba Waba ya ce sun rubuta wa gwamnatin Kaduna takarda tun kusan mako biyu domin neman zama a kan teburin sulhu da kuma lalubo bakin zaren matsalar.
"Kusan makonni biyu na tura wa Gwamnatin El-Rufa'i takarda domin jin ina aka kwana, har yau ba mu da tabbacin ko takardar ta isa wurinsa," in Kwamred Waba.
A cewarsa suna da takardun duka ma'aikatan da aka kora a fadin jihar ba bisa ka'ida ba.
Ya musanta zargin da ake yi na cewa ma'aikatan bogi ne ake kora, yana cewa babu wanda ba shi da takardar daukar aiki a hannunsa.
A watan da ya gabata ne Kungiyar kwadago ta NLC reshen jihar ta ce ya zuwa watan Afrilu gwamnatin jihar ta kori ma'aikata kusan dubu uku daga bakin aiki.
Kungiyar ta yi ikirarin cewa ma'aikatan waɗanda galibi kanana ne an sallame su ba tare da wani kwakkwaran dalili ba, inda ta bayyana rashin amincewarta tare da yin barazanar fara daukar mataki a kan lamarin muddin gwamnati ba ta sauya shawara ba.
Gwamnatin Rl-Rufa'i dai ta sha kai ruwa rana da ma'aikata, musamman malaman makaranta wadanda a baya ta kori wasu daga cikinsu.