You are here: HomeAfricaBBC2021 05 12Article 1259560

BBC Hausa of Wednesday, 12 May 2021

Source: BBC

Mutuwar wani mutum a cocin Najeriya ta sa yin gargadi kan amfani da turaren tsarkake ruhi

Mambobin cocin na zuwa ne da turarensu amma kuma ana iya saya a cikin cocin Mambobin cocin na zuwa ne da turarensu amma kuma ana iya saya a cikin cocin

Mutuwar wani mutum saboda wuta da ta tashi sakamakon kyandir da aka kunna da fesa turaren tsarkake ruhi lokacin yin addu'a ta sa daya daga cikin manyan majami'un da ke Najeriya yin gargadi.

Cocin Celestial da mambobinta ke saka fararen kaya kuma suke zuwa ibada babu takalmi a kafarsu, sananne ne a kudu maso yammacin Najeriya amma yana da rassa a duk fadin kasar da kasashen waje.

Kayode Badru yana addu'a da kyandir lokacin wani taron addu'oi da aka shirya masa a majami'ar ranar Litinin din da ta gabata lokacin da lamarin ya faru.

Dattawa a cocin sun ta yi wa Badru addu'a kuma ana tunanin malamin cocin da ke jagorantar addu'o'in ya fesa masa turare mai tsarki abin da ya sa wuta ta tashi saboda wani kyandir da ke kusa.

Nan da nan wutar ta mamaye Mr Badru wanda yake sanye da fararen tufafi wadanda yawanci ana yin su ne daga yadudduka masu saurin kamawa da wuta.

Ya mutu a asibiti ranar Alhamis sakamakon kunar da ya samu a jikinsa.

Imolemitan Ojo, wani babban fasto a cocin, ya fada wa BBC Pidgin cewa 'yan sanda sun kama malamin da ya jagoranci taron addu'o'in da wasu manyan da suke wajen lokacin da abin ya faru.

Ana gudanar da addu'oi ne da kyandir da ke kunne da kuma turare abin da ke nuna haske da kuma kyakkyawan yanayi.

Mambobin cocin na zuwa ne da turarensu amma kuma ana iya saya a cikin cocin.

Ba wai an tsara a rika fesa turaren ba ne fiye da kima sannan ana shawartar mambobin su rika sirka shi da ruwa. Sai dai babu masaniya ko an yi wa Mr Badru hakan.

Wata sanarwa daga cocin ta tunatar da mambobi cewa "an tsara a rika fesa ko yayyafa ko kuma zuba turaren tsarkake ruhin da kyandir da aka kunna."

"Fesa shi ko zuba turaren da ba a sirka da ruwa ba ga kuma kyandir mai ci wata al'ada ce da aka aro ba wai ta samo asali ba ne da daga 'yan cocin Celestial," in ji sanarwar.

Rahotanni sun ce Mr Badru, wani mai kudi ne dan Najeriya da ke Dubai ya je cocin ne domin bikin nuna godiya.

Wani rahoton kuma ya ce yana Najeriya ne domin halartar bikin yaye mutum 40 da ya dauki nauyin karatunsu.

Cocin na Celestial da Rabaran Samuel Bilehou Oshoffa ya kafa a 1947 a Porto-Novo da ke Benin, a yanzu yana da rassa a duka fadin duniya.