You are here: HomeAfricaBBC2021 05 12Article 1259413

BBC Hausa of Wednesday, 12 May 2021

Source: BBC

Kelechi Iheanacho: Wilfred Ndidi da ni ba mu taɓa yanke ƙauna kan ƙwazona ba

Kelechi Iheanacho, dan wasan Leicester da Najeriya Kelechi Iheanacho, dan wasan Leicester da Najeriya

Dan wasan Leicester da Najeriya Kelechi Iheanacho wanda ya dawo kan ganiyarsa ya dage cewa bai taba karaya ba game da yiwuwar komawa kan ganiyar tasa ko da kuwa a lokacin da duniya ta juya masa baya.

Iheanacho, mai shekara 24, bai samu gayyata daga Najeriya ba domin buga wasannin karshe na gasar cin Kofin Nahiyar Afirka ta 2019 Afirka bayan da ya tsinci kansa a tsaka mai zuwa a kungiyar kwallon kafar Leicester.

A watannin baya bayan nan lamura sun sauya game da shi inda aka ayyana shi a matsayin Gwarzon dan wasan kwallon kafar gasar Firmiya na watan Maris, kuma ya tsawaita zamansa a Leicester zuwa 2024 haka kuma yana kan hanyar samun kyauta biyu a watan Afrilu.

Ya shaida wa BBC Sport Africa cewa: "Ina ganin mutane da dama suna ganin ba ni da muhimmanci, amma ban taba yin kokwanto kan kwarewata ba."

"Na shiga mawuyacin hali lkaci da koma ya tabarbare mini.

"Amma na yi aiki tukuru, kuma ina da manaja da sauran ma'aikata a Leicester, sai dai abu mafi muhimmanci ina tare da dan uwa kuma abokina Wilfred [Ndidi] wanda ya rika karfafa mini gwiwa.

"Na yi matukar fuskantar kalubale amma yanzu ina cikin farin ciki komai ya sauya mini."

Iheanacho shi ne dan kwallon da ya fi zura wa Leicester a kakar wasa ta bana inda ya ci mata kwallaye 18.

Cikin wadanda suka soki Iheanacho har da kocin Najeriya Gernot Rohr wanda a bainar jama'a ya nuna kokwantonsa game da kwazon dan wasan da kwarewarsa a 2019.