You are here: HomeAfricaBBC2021 04 30Article 1246984

BBC Hausa of Friday, 30 April 2021

Source: BBC

Arsenal tana da damar kai wa wasan karshe a Emirates

Villareal ta yi nasarar doke Arsenal da ci 2-1 a wasan farko zagaye Villareal ta yi nasarar doke Arsenal da ci 2-1 a wasan farko zagaye

Villareal ta yi nasarar doke Arsenal da ci 2-1 a wasan farko zagaye daf da karshe a Europa League da suka fafata a Spaniya ranar Alhamis.

Minti biyar da fara tamaula Villareal ta ci kwallo ta hannun Manu Trigueros, sannan Raul Albiol ya kara na biyu tun kan su je hutun rabin lokaci.

Arsenal ta karasa wasan da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Dani Ceballos jan kati.

Arsenal ta zare kwallo daya ta hannun Nicolas Pepe da hakan ya kara mata karfin gwiwa cewar za ta iya kai wa wasan karshe a mako mai zuwa a Ingila.

Saura minti 10 a tashi daga wasan Etienne Capoue na Villareal ya karbi katin gargadi na biyu da hakan ya sa aka yi masa jan kati a fafatawar.

Golan Arsenal, Bernd Leno ya yi kokari sosai, bayan da ya hana kwallo biyu shiga raga da hakan ya kara karfin gwiwar 'yan wasan Gunners.

Wannan shi ne karon farko da kungiyoyin biyu suka kara a Europa League, wanda Villareal ta yi nasara.

Tun a baya sun fafata sau hudu a Champions League, inda Arsenal ta yi nasara a biyu da canjaras biyu, kuma Gunners ba ta taba cin Villareal a Spaniya ba.

Ranar 6 ga watan Mayu Arsenal za ta karbi bakuncin Villareal a wasa na biyu, domin fitar da wadda za ta kai karawar karshe a gasar bana.

Arsenal wadda take ta 10 a teburin Premier da saura wasa biyar-biyar a karkare kakar bana tana fatan lashe kofin domin ta samu buga gasar Zakarun Turai ta badi cikin ruwan sanyi.