You are here: HomeAfricaBBC2021 04 29Article 1246069

BBC Hausa of Thursday, 29 April 2021

Source: BBC

Majalisar Najeriya na yunƙurin tabbatar da ƙarin kujeru ga mata

Nigeriya na bin tsarin wasu kasashen Akrika kaman Kenya da Uganda Nigeriya na bin tsarin wasu kasashen Akrika kaman Kenya da Uganda

'Yan majalisar dokokin Najeriyar sun fara wani babban mataki na tabbatar da karin mata a kujerun majalisa.

Idan kudirin ya zama doka, majalisar dattijan Najeriya zata kasance tana da mata 37, yayin da wakilai zata kasance tana da mata 74.

Kudirin dokar da ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai zai sa a yi wa kundin tsarin mulkin shekarar 1999 kwaskwarima domin ƙirƙirar sabbin kujerun majalisar dokoki da aka kebe wa mata .

Kudirin da Mataimakin mai tsawatarwa, Nkeiruka Onyejocha na jam'iyyar PDP daga Abia da wasu 'yan majalisa 85 suka dauki nauyin, an yi muhawara akansa kafin daga bisani aka amince da shi .

Kudirin ya bayar da shawarar ƙirƙirar ƙarin kujerar sanata guda a kowace jiha ta tarayya da Abuja.

Mata ne kawai za su mamaye kujerar.

A yanzu kowace jiha ta Najeriya tana da kujerun majalisar dattawa uku yayin da Abuja ke da guda ɗaya.

Duk da cewa duk wani da ya cancanta zai iya tsayawa takarar kujerar sanata, amma fani ne da maza suka yi wa babakere inda takwas daga cikin sanatoci 109 na yanzu mata ne.

Kudirin ya kuma nemi ƙirƙirar sabbin kujerun majalisar tarayya biyu a kowace jiha da kuma Abuja wadanda za a ware wa mata. A yanzu haka Najeriya tana da kujerun majalisar tarayya na wakilai 360 a majalisar wakilai, inda 13 daga cikinsu ne a yanzu mata.

Kudirin na da niyyar sauya sashe na 48, 49, 71, 77, 91 da 117 na kundin tsarin mulkin Najeriya.