You are here: HomeAfricaBBC2021 04 23Article 1240291

BBC Hausa of Friday, 23 April 2021

Source: BBC

Benzema ya ci kungiya 35 da ya kara da su a La Liga

Karim Benzema, dan kwallon Real Madrid Karim Benzema, dan kwallon Real Madrid

Karim Benzema ya ci gaba da kafa tarihi a wasannin da yake buga wa Real Madrid, wannan karon a fanni cin kungiyoyi 35 da ya hadu da su a La Liga.

Ranar Talata Real ta doke Cadiz da ci 3-0 a gasar ta Spaniya, kuma Benzema ne ya ci biyu a karawar da ta kai ya zura 21 jumulla a kakar bana.

Wannan bajintar ta sa ya zama na farko da ya zura kwallo a dukkan kungiyoyi 35 da ya hadu da su a gasar La Liga.

Da wannan sakamakon Real Madrid ta koma ta daya a kan teburin La Liga da maki 70 iri daya da na Atletico wadda za ta karbi bakuncin Huesca ranar Alhamis.

Benzema ya buga wasa 377 a La Liga a Real Madrid tun daga lokacin da ya fara yi mata tamaula ranar 29 ga watan Agustan 2009 da ya fara cin Deportivo La Coruna.

Kawo yanzu ya ci kwallo 190, shi ne na hudu a jerin wadan da suke kan gaba a ci wa Real Madrid kwallaye a tarihin gasar La Liga.

Kungiyoyi 35 da Benzema ya ci ko dai kwallo daya ko fiye da haka sun hada da Granada da Getafe da Malaga da Rayo da Athletic da Betis da Sevilla da Barcelona da Real Sociedad da Deportivo da Valencia da Espanyol da Racing da kuma Osasuna.

Sauran sun hada da Villarreal da Almeria da Mallorca da Eibar da Atletico da Sporting da Tenerife da Herrcules da Celta da Valladolid da Alaves da Levante da Girona da Zaragoza da Las Palmas da Xerez da Elche da Cordoba da Huesca da Leganes da kuma Cadiz.