You are here: HomeAfricaBBC2021 04 23Article 1240300

BBC Hausa of Friday, 23 April 2021

Source: BBC

Brazil da Jamus na rukuni daya a tamaular Olympic a Japan

Za a fara wasannin Olympics ranar 22 ga watan Yuli kwana daya kan bikin bude gasar Za a fara wasannin Olympics ranar 22 ga watan Yuli kwana daya kan bikin bude gasar

Mai rike da kambun tamaula a Olympic, Brazil tana rukuni daya da Jamus a jadawalin da aka fitar ranar Laraba, domin fafatawar da za a yi a Japan.

Sauran tawagaogin da ke rukuni na hudu, sun hada da Ivory Coast da kuma Saudi Arabia.

Mai masukin baki Japan, wadda ta ci lambar yabo ta tagulla a 1968 tana rukunin farko da ya kunshi Faransa da Afirka ta Kudu da kuma Mexico.

Rukuni na uku ya hada da Masar da Spaniya da Argentina da kuma Australia, inda rukuni na biyu ke dauke da Korea ta Kudu da New Zealand da Romania da kuma Honduras.

Za a fara wasannin ranar 22 ga watan Yuli kwana daya kan bikin bude gasar, wadda aka daga a 2020, sakamakon bullar cutar korona.

A jadawalin fafatawar mata kuwa, mai rike da kambu kashi hudu wato Amurka za ta kara a rukunin da ya hada da Sweden da Australia da kuma New Zealand.

Mai masaukin baki Japan tana rukunin da ya hada da Burtaniya da Canada da kuma Chile.