You are here: HomeAfricaBBC2021 04 12Article 1230910

BBC Hausa of Monday, 12 April 2021

Source: BBC

Najeriya: Majalisar Dinkin Duniya za ta rage ayyukan jin kai a Damasak

Edward Kallon ne Babban Jami'in ayyukan jin ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya Edward Kallon ne Babban Jami'in ayyukan jin ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya

Babban Jami'in ayyukan jin ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya ya sanar da rage ayyukan ba da agaji a yankin Damasak sakamakon mummunan harin da ake zargin ƙungiyar Boko Haram ta kai a ƙarshen mako.

Mista Edward Kallon ya dai yi alla-wadai da harin wanda ya yi sanadin ƙona ofisoshin ƙungiyoyin ba da agaji uku a garin Damasak.

Ya nuna damuwa a kan cewa ayyukan jin kai da za a rage a yankin zai shafi mutun sama da dubu dari takwas da suka rasa muhallinsu da dubbai da ke samun mafaka a wasu yankuna.

Rahotanni sun ce baya ga dukiyar da aka ƙona, an kuma kashe aƙalla mutum takwas yayin wannan hari ciki har da jami'an tsaro.

Kafar watsa labarai ta PR Nigeria ta ce mayakan Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya biyu a harin kwantar baunar da suka kai mu su a yankin lokacin da suke kokarin cafke wani da ke kai wa Boko Haram bayani.

Damasak cibiyar gudanar da ayuykan jin kai ce a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.