You are here: HomeAfricaBBC2021 04 12Article 1230868

BBC Hausa of Monday, 12 April 2021

Source: BBC

Prince Philip: Dangantakar Philip da iyalansa

Yarima Philip tare da Sarauniyar Ingila Yarima Philip tare da Sarauniyar Ingila

Saukin Kan Philip ya sa Iyalansa Ke Matukar Kaunarsa.

Yanzu matarsa ta zama shugabarsa, kuma shugabar jama'a, duk da cewa a sha'anin rayuwa ta dara ta a komai.

Amma fa a rayuwarsa ta gida abin ba haka yake ba. Ya kasance yana yawan cewa, ''Inda a ce gidan Sarautar Birtaniya Kamfani ne, to sarauniya a matsayinta na babbar Darakta, ba ta taba yanke hukunci ba, ba tare da shawarar shugabanta ba.''

'Ya'yansa na matukar nuna masa kauna. Duk da cewa ana kallon sa a matsayin shugaba mai zafi, amma yana da sanyi a rayuwarsa ta gida, musamman ma idan yanan cikin iyalina. ''Yana son su, suma suna son sa.''

Marigayi Kwamandan Sojojin Ruwa na Bama ya taba gayawa marubuci Gyles Brandreth cewa, ''Babu shakka Philip mutum ne mai matukar tausayin 'ya'yansa, musamman ma lokacin da suke kanana.''

Sai dai kuma Mai martaba Duke ya ci gaba da ruwa irin ta dogaro da kai da tsawa akan abin da yake das hi, Duk da irin kykkyawar alakar da yake da ita tsakaninsa da sauran Gidajen Sarautar Turai amma ya wadatu da kansa,

Rayuwar Mai martaba Philip a lokacin da yake yaro karami na cike da tawali'u. An haife shi a Corfu daga Masarautar Folklore ta kasar Girka.

An kori mahaifinsa daga kasar Girka lokacin da Philip bai wuce danyaye ba, don haka a matsayinsa na karamin yaro ya rayune a hannun 'yan Birtaniya dake yankin teku, a cikin wani sunduki mai launin rowan lemo. Mahaifiyarsa ta hadu da lalurar tabin hankali, hakan ya sa mahaifinsa ya yi hijira zuwa Kudancin Faransa tare da wata farkarsa.

Yarima ya yi rayuwa ta yarinta ne tsakanin makarantar yamma da yake zuwa tare da yaran sojoji da kuma yankin teku da yake rayuwa ba uwa ba uba.

Rikicinsa da Charles

Philip ya rayu tare da sauran yayyensa mata su hudu, ya shaku das u matuka, kuma shi ne kadai namiji a gidansu. Ya hadu da wani mummunan tashin hankali lokacin da daya daga cikin yayyen nasa mai suna Cecilie ta rasu a hadarin jirgin sama a shekarar 1937.

Kasancewar Philip bas hi da dangin da zai ziyarta lokacin hutu, ya je ya tare a wata makaranta dake arewacin Scotland, inda ya rika jin cewa da rayuwar makaranta da ta gida duk daya ne a wajensa.

A nan ya samu dabi'ar Kadaita-Kai, da shiru-shiru, da kuma rashin damuwa da al'amuran jamaa, wannan dabi'a ita ta haifar masa da matsala tsakaninsa da babban dansa.

Za'a iya cewa, yayin da kalubalen rayuwa da Philip ya hadu da shi a rayuwar da ya yi a Gordonstoun ya zama ceto a gare shi a matsayinsa na wanda bas hi da kowa, sai gas hi dansa Charles day a taso cikin gata ya zama fandararre.

Duk da Kyakkyawar niyyar da Philip yake da ita ga dansa, kuma duk da cewa babu wata tarbiyya da ya gada daga iyayensa, amma dai ya yi kokarin ganin dansa ya zama shiryayye.

Wani marubuci da ake kira Jonathan Dimbleby a cikin tarihin rayuwar Charles day a rubuta, ya ce, Halayyar Philip a matsayinsa na wanda ya yi rayuwar kadaici da yi wamtane tilas, ta say a yiwa dansa auren dole tare da tirsasa shi ya yi rayuwar kadaici irin ta gidan sarauta.

Dukkanin su, da uban da dan, sun sha wahalar juna matuka, saboda bancin ra'ayin da ke tsakanin su. Har ta kai ga uban yana fadin cewa, ''don kawai ina daukar dukkanin al'amurana da muhimmanci, shi ya sa ake min kallon Mai tsattsauran hali.''

Kyakkyawar Fahimta

Mai martaba Duke, kamar dai yadda ya saba fadi a duk lokacin da yake fuskantar wata matsala a rayuwarsa, ya ce, ''Mutane bas a yi min adalci a irin fassarar da suke yi min a rayuwa, amma dole a haka zan hakura.''

Dangantakarsa da sauran 'ya'yansa ta fi kyau fiye da ta babban dansa. Domin ya shawarci dansa Yarima Andrew kuma Duke na York day a shiga aikin sojan ruwa, sannan ya bi duniya a sannu, sai ya amince da shawarar.

Kuma lokacin da dan nasa yi murabus daga aikinsa a tashar jiragen ruwa, 'yan jarida sun ta yayata maganar cewa, an samu sabani a cikin iyalin gidan sarauta, amma abin bah aka yake ba.

Irin wannan tausayi ne ya nuna a lokacin jana'izar Gimbiya Diana, lokacin da 'ya'yanta biyu suka yi tsaye akan gawarta suna tunanin su tashi su raka gawar zuwa makabarta ne ko kuwa su yi zamansu.

Yarima, wanda da farko bai yi niyar bin gawar ba, amma day a fahimci halin da jikokin nasa suke ciki, sai ya je kusa da William y ace das hi ''Idan har ba ka raka gawar nan ba, to za ka yi nadama anan gaba, idan ni na bi 'yan daukar gawa za ku biyo ni?''

Mutumin da shi bai rayu tare da iyayensa ba, amma ya samu kwanciyar hankali da bai taba zaton zai same shi a aurensa da Elizabeth ba.

Dogaro da kai da kawaici day a tashi das hi tun yana yaro, ya sa a wani lokaci ana yi masa kallon mutumin da bai damu da rayuwar iyalinsa ba.

Amma aminansa sun ce ko kadan bah aka rayuwarsa take ba. A cikin littafin da Gyles Brandreth ya rubuta mai suna Philip da Elizabeth: Hoton Rayuwar Auren Saraki, ya tambayi Mai martaba Duke game da dangantaka tab a-saban-ba da ake gani tsakaninsa da 'ya'yansa? Sai y ace ''Mu iyali ne fiye da yadda kake tsammani.''

A gaskiya ma dai, sha'awar da Edwar ya yin a barin aiki ya dawo kusa da mahaifinsa, ya kara sawa sun shaku matuka. Kuma kamar sauran yara, Edward ya cigaba da zama mai biyyya ga umarnin mahaifinsa.

Game da 'yarsa Anne kuwa, a nan Mai martaba Duke ya samu mai hali irin nasa, duk da cewa gimbiyar takan bayyanawa mahaifinta ra'ayinta, amma dai akwai kyakkyawar fahimta a tsakaninsu.

Sai dai ta fahimci cewa, wani lokaci idan suna tattaunawa da uban, ta yi shiru kada ta sake cewa uffan shi ya fi.

Kasancewar Mai martaba Duke ya sami gagarumin goyon baya da hadin kan jamaa a tsawon shekarun aurensa, da ace kan 'ya'yansa a rabe yake, to da hakan zai rage masa darajar da yake da ita a idon jamaa.

Aiki Da Hankali

Har ila yau ya baiwa sirikarsa Gimbiya Diana ta Wales cikakken goyon baya a lokacin rikicin aurenta da mijinta Charles. An kuma fahimci matukar kusacin dake tsakaninsu a cikin wasikun da yake rubuta mata, inda a kowacce wasika yake faraway da ''Zuwa ga 'yata'' kuma an baje wasikun domin jamaa su gani a lokacin da ake binciken musabbabin mutuwarta.

Wasikun, wadanda aka rubuta a 1992 lokacin da aurenta da Charles ya shiga rudani, sun nuna matukar tausayi da Mai martaba Duke ya nuna mata, tare da jaddada niyarsa a kodayaushe na ganin auren ya dore.

''Zan yi matukar kokarina na taimaka miki ked a Charles, duk da cewa ni ba kwararre ba ne a fannin sasanta ma'aurata.''