You are here: HomeAfricaBBC2021 04 09Article 1227772

BBC Hausa of Friday, 9 April 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Rice, Aguero, Mbappe, Vazquez, Haaland, Dembele, Coutinho

Kylian Mbappe, dan kwallon PSG Kylian Mbappe, dan kwallon PSG

Manchester United za ta duba yuwuwar musayar dan wasan Ingila na tsakiya Declan Rice, mai shekara 22, da West Ham a madadin Jesse Lingard, mai shekara 28, wanda ke zaman aro daga United din. Jaridar Athletic ta ruwaito labarin.

Leeds United ta shiga layin kungiyoyin da ke tururuwar daukar dan wasan Manchester City na gaba, Sergio Aguero, dan Argentina mai shekara 32, wanda yarjejeniyarsa da City za ta kare a karshen kakar bana. Labarin ya fito ne daga 90min.

Zaman tauraron dan wasan gaba na Faransa Kylian Mbappe a Paris St-Germain ya kasance ba tabbas, kasancewar gwanin mai shekara 22 na ci gaba da watsi da duk wani tayi na kulla sabuwar yarjejeniyar zama a kungiyar ta birnin Paris. Labarin na cikin jaridar Telegraph.

Mbappe ya ki sanya hannu don ci gaba da zama a PSG din ne saboda yana son tafiya Real Madrid. Jaridar Cuatro ta Sifaniya ce ta ruwaito.

Ita kuwa Real Madrid din tuni ta yanke shawarar amfani da dan wasan gaba na Brazil Vinicius Junior, mai shekara 20, domin musayarsa da Mbappe a bazaran nanr. Ruwayar El Chiringuito, daga jaridar Metro.

Haka kuma dan wasan Real Madrid din Lucas Vazquez, mai shekara 29, dan kasar Sifaniya, wanda yarjejeniyarsa za ta kare a karshen kakar nan da ake ciki, ya ki sabunta zaman nasa a Bernabeu saboda sha'awarsa da Manchester United da Chelsea ke yi. Jaridar Sun ce ta kawo labarin.

Mai yuwuwa Chelsea ta yi kokarin sayen dan wasan Borussia Dortmund na gaba Erling Braut Haaland, dan Norway mai shekara 20, da kuma na Manchester City Aguero a lokacin kasuwar sayen 'yan wasa ta bazara da ke tafe. Ruwayar 90min.

Lyon ta sanya farashin fam miliyan 25 a kan dan was anta na baya Joachim Andersen, dan kasar Denmark mai shekara 24, wanda a yanzu yake zaman aro a Fulham. Rahotanni na cewa Manchester United da Tottenham na dubu yuwuwar sayensa. Labari daga Metro.

Dan wasan gaba na gefe, Takumi Minamino, na kasar Japan mai shekara 26, y ace yana matukar mamakin yadda Liverpool ta yanke shawarar bayar da shi aro ga Southampton a watan Janairu. Jaridar Independent ta labarto.

Haka kuma kungiyar ta Southampton na tattaunawa domin tsawaita zaman dan wasan Ingila na gaba Theo Walcott a kungiyar. Dan wasan mai shekara 32 a yanzu yana zaman aro ne na shekara daya daga Everton. Ruwayar jaridar Southern Echo.

Liverpool na shirin sayen dan wasan tsakiya na kungiyar AZ Alkmaar Teun Koopmeiners mai sheakar 23, dan kasar Holland a matsayin wanda za ta iya amfani da shi wajen maye gurbin Georginio Wijnaldum, shi ma dan Holland mai shekara 30.Jaridar AS ta Sifaniyanci ce ta ruwaito.

Kociyan Brighton Graham Potter y ace yana matukar sha'awar tsawaita zaman dan wasan gaba na Ingila Danny Welbeck a kungiyar, amma ba za su tattauna kan batun ba sai a lokacin bazara. A watan Yuni ne yarjejeniyar zaman dan wasan mai shekara 30 za ta kare a kungiyar. Sky Sports ta ruwaito labarin.

Dan wasan tsakiya na Chelsea kuma dan Italiya Jorginho mai sheakara 29, ya ce yana son komawa tsohuwar kungiyarsa Napoli kafin ya yi ritaya daga wasan kwallon kafa. Sky Sport ta ruwaito.

Dan wasan gaba na Faransa Ousmane Dembele, mai shekar 23, ya amince ya sanya hannu a sabuwar yarjejeniyar ci gaba da zamansa a Barcelona. Jaridar Marca ta Sifaniya ce ta labarto.

Sai dai kuma tsohon dan wasan tsakiya na Liverpool, kuma dan Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 28, na daga cikin 'yan wasan da Barcelonar za ta sayar a kasuwar bazara mai kamawa.Jaridar Mirror ta ruwaito.

Haka kuma jaridar ta Mirror ta ruwaito cewa dan wasan gefe na Brazil Willian, mai shekara 32, na da kudurin ganin ya dawo kan ganiyarsa tare da taka rawar-gani a Arsenal duk da koma-bayan da ya samu a kakarsa ta farko a kungiyar bayan da ya koma can daga abokiyar hamayya Chelsea.