You are here: HomeAfricaBBC2021 04 07Article 1225651

BBC Hausa of Wednesday, 7 April 2021

Source: BBC

Matsalar tsaro a Najeriya: 'Yan bindiga sun kashe mutum 8 a jihar Kaduna

Rahotanni sun nuna ce wa wasu 'yan bindiga sun harbe akalla mutane takwas Rahotanni sun nuna ce wa wasu 'yan bindiga sun harbe akalla mutane takwas

Mahukunta a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya sun ce wasu 'yan bindiga sun harbe akalla mutane takwas tare da jikkata da dama a wasu hare-hare da suka kai kan wasu kauyuka.

Kwamishinan tsaro na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya ce a daya daga cikin hare-haren da aka kai ranar Talata, mutanen dauke da makamai sun toshe wata babbar hanyar da ke kusa da kauyen Kadanye a yankin Kajuru - inda suka bude wuta a kan wata motar bas da wata babbar mota suka kashe mutane biyar.

Wasu rahotanni sun nuna cewa an kuma sace mutane da yawa yayin harin.

Yayin zantawa da BBC, kwamishinan ya ce huɗu daga cikin mutanen da aka kashe masu saran itace ne a dazuka, sai kuma wani direban bas, da ke ɗaukar fasinjoji a wata mujami'a da ke garin Zaria.

Samuel Aruwan ya ƙara da cewa; ''har ila yau mun samu labari daga jami'an tsaro cewa 'yan fashin dajin sun kuma farwa garken wani makiyayi a unguwar 'yan Doho da ke ƙaramar hukumar ta Kachia, suka kashe shi, sannan suka sace shanunsa kusan 180.

Mahukunta a jihar dai sun ce da alama 'yan fashin dajin sun fara canja salo ne daga mayar da hankali kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Najeriya na fama da matsalolin tsaro wadanda suka hada da yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da kungiyoyin masu dauke da makamai ke yi, da rikicin Boko Haram da kuma rikicin 'yan awaren Biafra a yankin kudu maso gabashin kasar inda ake ci gaba da fuskantar hare-hare kan jami'an tsaro da wurarensu.

A ranar Litinin wasu mutane dauke da muggan makamai suka kutsa kai cikin wani babban gidan yari, inda suka tayar da bama-bamai tare da sakin sama da fursunoni 1800 a garin Owerri a yankin.

Fursunonin da har yanzu ba a ga yawancinsu ba.

Kwana guda bayan kai wannan hari, maharan sun sake kai wani sabon harin kan wani ofishin 'yan sandan a dai wannan jiha ta Imo, tare da kone motoci da ginin ofishin, ko da yake ba su kashe jami'i ko daya ba.