You are here: HomeAfricaBBC2021 04 06Article 1225534

BBC Hausa of Tuesday, 6 April 2021

Source: BBC

Jihar Imo: ''Akwai siyasa a batun hare-haren da ake kai wa jami'an tsaro a kudancin Najeriya''

Hare-hare ya yawaita akan jami'an tsaro a wasu jihohin kudancin Najeriya a baya bayan nan Hare-hare ya yawaita akan jami'an tsaro a wasu jihohin kudancin Najeriya a baya bayan nan

Masana tsaro a Najeriya sun fara tsokaci dangane da yawaitar hare-haren da mahara ke kai wa kan jami'an tsaro a wasu jihohin kudancin Najeriya a baya bayan nan.

Ranar Litinin ne hukumar kula da gyaran hali ta Najeriya ta ce 'yan bindiga sun kubutar da fursunoni 1,844 daga gidan yarin birnin Owerri na jihar Imo, jim kadan bayan bankawa sashen binciken laifuka na rundunar yan sandan jihar wuta.

Wannan al'amari na zuwa ne kwanaki kalilan, bayan da rundunar yan sandan Najeriya ta ce yan kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra wato IPOB ne ke kai wa jami'anta hare hare a wasu jihohin kudancin Najeriyar.

Wani masanin harkokin tsaro a Najeriya Malam Kabiru Adamu daga kamfanin Baecon Consultancy, ya ce awai alamun cewa siyasa ta shiga wannan al'amari, kuma wasu ne ke yin amfani da wannan dama domin aiwatar da burinsu na tayar da yamutsi a Najeriya, alabashi sai su cimma manufofinsu.

A cewar kwararren ''wadannan hare hare sun fara ne tun watan ɗaya har zuwa yanzu, kuma alkaluman da muke da su na nuna cewa an kai wa jami'an tsaro hari dai-dai-dai har guda 40. kuma dukkansu a kan jami'an tsaro, ko a kashe su a kwace makamansu, ko a kona wuraren aikinsu''.

Ya ƙara da cewa akwai bukatar hukumomin tsaron Najeriya su inganta ahanyoyinsu na tattara bayanai, ganin yadda tuni duniya ta ci gaba, don haka matsawar ana son kawo karshen wannan matsala toh dole ne a rungumi hanyoyin zamani.

Sufeto Janar na 'yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu ya ba da umarnin aikewa da wasu karin 'yan sandan kwantar da tarzoma zuwa Jihar Imo, inda aka ƙona ofishin 'yan sandan a safiyar Litinin 5 ga watan Afrilun 2021.

Kazalika, rundunar ta ce binciken farko-farko da ta gudanar ya nuna cewa 'yan bindigar da suka kai harin mambobin ƙungiyar IPOB ne masu fafutikar ɓallewa daga Najeriya tare da kafa ƙasar Biafra.