You are here: HomeAfricaBBC2021 04 06Article 1225507

BBC Hausa of Tuesday, 6 April 2021

Source: BBC

Abin da ya sa kamfanin LG zai daina kera wayoyin hannu

LG zai daina kera wayoyin salula da yake tafka asara a kai LG zai daina kera wayoyin salula da yake tafka asara a kai

Kamfanin kera kayan lataroni LG ya bayyana a ranar Litinin cewa zai daina kera wayoyin salula da yake tafka asara a kai.

A cikin watan Janairu ne katafaren kamfanin lataronin na kasar Korea ta Arewa ya ce yana duba duka zabin da yake da shi bayan shafe kusan shekaru shida yana tafka asarar da ta kai $4.5bn.

Kamfanin na LG ya kirkiri abubuwa daban-daban da suka hada da na'urorin daukar hoto, da ya kai ga zama mafi girma wajen kera wayoyin salula a shekarar 2013.

Amma shugabannin sun ce kasuwar wayoyin salular ta kasance ''ike da gagarumar gasar kasuwanci".

Yayin da kamfanonin kera kayan lataroni na Samsung da Apple ne manyan masu tashe a kasuwar wayoyin salular, LG ya gamu da cikas na matsalolin da suka shafi manhajojin sarrafa wayoyinsa.

Bayan da LG din ke fama da asarar da ya tafka, ya gudanr da tutuba da tattaunawa game da sayar da wani bangare na kasuwancin na shi, amma haka ba ta cimma ruwa ba.

Har yanzu yana mataki na uku cikin masu tashe a Amurka ta Arewa amma tagomashinsa ya yi kasa a sauran kasuwanni.

A cewarsa: "Matakin LG na yanke shawarar na ficewa daga kasuwar bangaren wayoyin salula zai bai wa kamfanin damar mayar da hankali a wuraren da zai bunkasa bangarori kamar na kayan lataroni na motoci, da mutum-muutmi, da gidajen tafi-da gidanka."

Kamfanin ya yi ta kirkirar wayoyin don fafatawa da sauran kamfanoni manyan abokan gasar shi, bayan da a bara ya kaddamar da wata samfurin wayar mai mai fadin fuska.

Motoci masu aiki da lantarki da akwatunan Talabijin

Har yanzu LG na da kasuwancin lataroni mai karfi, musamman na kayyainin lataroni na amfanin gida da akwatunan talabijin.

LG shi ne na biyu mafi girma wajen sayar da akwatunan talabijin baya ga Samsung.

A cikin watan Disamba ne ya kaddamar da bikin hadin gwuiwa da kamfanin Magna International mai kera motoci da zai rika kera masu kayyakin hada motoci masu aiki da lantarki.

Za a cigaba da sayar da sayar da wayoyin salular na LG, kana zai rika samar da bayani game da manahjojinta ga masu saye.

Ana sa ran kamfanin zai rufe bangaren a karshen watan Yuli.

"Nan gaba kadan, LG zai ci gaba da amfani da kwarewarsa a fannin kera wayoyin salular ya kirkiri fasaha mai alaka da sufuri don kara karfin gasar kasuwanci a sauran bangarorin kasuwancinsa," a cewar mai magana da yawun kamfanin.

Masu sharhi sun ce akwai yiwuwar abokan gasar kamfanin na LG wato Samsung da kamfanonin kasar China kamar su Oppo, da Vivo da Xiaomi za su amfana da ficewar kamfanin na LG.

Masu kera wayoyin tafi-da-gidanka sun sha fama a lokacin barkewar annobar korona da ya haifar da koma-baya ga kasuwanci na kashi 10 bisa dari a shekarar 2020 a kasar saboda kullen da ya takaita bude manyan shaguna.