You are here: HomeAfricaBBC2021 04 06Article 1225486

BBC Hausa of Tuesday, 6 April 2021

Source: BBC

Yadda gurbatacciyar iska ke jawo kankancewar al’aurar maza

Wata kwararriya a fannin muhalli ta yi gargadi a cikin wani sabon littafinta Wata kwararriya a fannin muhalli ta yi gargadi a cikin wani sabon littafinta

Wata kwararriya a fannin muhalli ta yi gargadi a cikin wani sabon littafinta da ta yi bayani kan kalubalen da bil'adama ke fuskanta, cewa azzakari na kankancewa, yayin da 'ya'yan maraina na samun tawaya saboda gurbatacciyar iska.

A cikin littafin Dakta Shanna Swan, ta ce bil'adama na fuskantar abin da ta kira gagarumar matsalar rashin haihuwa sakamakon sinadarin phathalates, da ake amfani da shi a masana'antun yin robobi, wanda ya ke tasiri wajen lalata wasu daga cikin kwayoyin halittar dan adam.

A kan hakan ne Dakta Swan ta ce ana haifar jarirai masu dan karamin azzakari.

Littafin nata mai suna Count Down, ya yi bayani kan yadda ''zamani ke barazana ga karancin maniyyi, da haddasa wa mata da maza rashin haihuwa, da illa ga dan adam".

An fara binciken ne daga kan illar da sinadarin phthalate ke yi, wanda aka sanya beraye a inda sinadarin ya ke, an kuma gano akwai yiwuwar idan beraye suka shaki sinadarin za su haifi 'ya'ya da rashin karfin mazakuta.

Ta kuma gano jarirai maza da suka shaki sanadarin tun suna cikin mahaifiyarsu, za su samu tawayar al'aura abin da ke janyo kankantar shi.

Masana'antu suna samun sinadarin phthalates cikin sauki, wajen sarrafa abubuwa da dama, amma Dr Swan ta ce ana amfani da shi wajen yin robobi, da kayan wasan yara da mazuban abincin wanda a hankali su ke janyowa dan adam illa.

Sinadarin phathalates a hankali ya ke yin tasiri wajen hana sinadaran da ke sanya jikin dan adam girma, bincike ya kuma gano sinadarin ya na shafar bunkasar jima'i ga manya sai tawayar mazakuta ga yara.

Dakta Swan, wadda farfesa ce a fannin muhalli da kiwon lafiya a asibitin Mount Sinai da ke birni New York City na Amurka da take yawan bincike kan abubuwan da suka shafi illar da gurbacewar muhalli ke janyowa lafiyar dan adam.

Daya daga cikin binciken da aka wallafa a shekarar 2017, ya gano cikin shekaru 40 da suka gabata, bayan nazarin da aka yi kan bincike 185 da aka yi da ya shafi lafiyar maza 45,000.

Dakta Swan ta yi amanna da cewa, karuwar rashin haihuwa na nufin nan da shekarar 2045, maniyyin da maza ke fitarwa zai ragu matuka.