You are here: HomeAfricaBBC2021 04 06Article 1225480

BBC Hausa of Tuesday, 6 April 2021

Source: BBC

Shin ko jan katin da aka bai wa Neymar ne ya sakko da PSG daga saman Teburi

Neymar ya ture Djalo alkalin wasa yana zuwa ya basu jan kati. Neymar ya ture Djalo alkalin wasa yana zuwa ya basu jan kati.

An bai wa dan wasan Brazil da ke taka leda a Paris St-Germain jan kati a wasan da kungiyar ta yi da abokiyar hamayyarta Lille.

Lille ta doke PSG da ci daya mai ban haushi har gida, kuma nasarar ta ba ta damar darewa saman teburin gasar Ligue 1 tare da sakko da PSG da ke ta daya a baya.

Jonathan David mai shekara 20 ne ya jefa kwallo dayan da ta bai wa kungiyarsa wannan gagarumar nasara a minti na 20 da fara wasan.

Dan wasan PSG Neymar da na Lille Tiago Djalo duka sun samu katin gargadi da farkon wasan kafin daga bisani a basu jan kati su fita daga filin wasan a mintinan karshe.

Neymar ne ya ture Djalo bayan ya yi yunkurin yanka dan kwallon ya fadi sai kwallon ta fita waje sai Neymar ya ture Djalo alkalin wasa yana zuwa ya basu jan kati.

Neymar ya ci gaba da takalar Tiago da fada har lokacin da aka koresu daga filin wasan suka shiga dakin sauya kaya.

PSG na son daukar gasar Lig 1 ne karo na hudu a jere, sai dai yanzu sun koma na biyu da tazarar maki uku tsakaninsu da Lille da ke da maki 66.

Duk da cewa sun yi rashin nasara a wasanni biyun da suka buga na baya, yanzu sun dage sai sun dauki gasar wadda rabon su da ita tun 2010-11.

PSG ta yi rashin nasara a wasannin 10 da ta buga a duka wannan kakar wasanni, yanzu kuma za ta buga wasanta na gaba ne da Bayern Munich wadda suka buga wasan karshe tare na gasar zakarun Turai a ranar Laraba.