You are here: HomeAfricaBBC2021 04 05Article 1224046

BBC Hausa of Monday, 5 April 2021

Source: BBC

Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Mata, Haaland, Odegaard, Icardi, Winks, da De Gea

Dan kwallon Man United Mata Dan kwallon Man United Mata

Manchester United na shirin sabunta kwangialr dan wasan tsakiya na Sifaniya Juan Mata, mai shekara 32, da shekara daya. (Star)

Shugaban da ke kula da kwallon kafa Sebastian Kehl ya amince cewa watakila Borussia Dortmund za ta kai wani mataki wanda ba za ta iya ci gaba da rike dan kasar Norway mai shekara 20 Erling Haaland ba. (Goal)

Haaland ya sha gaban dan wasan Barcelona dan kasar Argentina Lionel Messi, mai shekara 33, a cikin jerin 'yan kwallon da Manchester City take son dauka duk da yake kocinta Pep Guardiola ya ce kungiyar ba za ta maye gurbin Sergio Aguero, mai shekara 32 ba. (Mirror)

An yi amannar cewa Haaland yana son tafiya Real Madrid amma kungiyar ta Sifaniya ba za ta yi yunkurin daukarsa ba har sai shi da kansa ya nuna sha'awar hakan kana ya nuna cewa zai bar Dortmund. (AS)

Watakila Arsenal ta sayar da matashin dan wasan Ingila Bukayo Saka, mai shekara 19, domin ta samu kudin sayen dan wasan Real Madrid dan kasar Norway Martin Odegaard, mai shekara 22, a mataki na dindindin, sannan ta sayi karin 'yan wasa domin yin garambawul a kungiyar. (Times - subscription required)

  • Liverpool na nuna damuwa kan Salah, Man Utd da Chelsea suna son Vazquez
Manchester United za ta biya golan Sifaniya David de Gea makudan kudade a matsayin kudin sallama a yayin da dan wasan mai shekara 30 yake shirin barin Old Trafford ia bazarar nan. (Mirror)

Kazalika Manchester United tana son dan wasan Paris St-Germain da Argentina Mauro Icardi, mai shekara 28 domin maye gurbin Edinson Cavani, mai shekara 34. (Teamtalk)

Atletico Madrid na sha'awar daukar dan wasan Tottenham da Ingila Harry Winks, mai shekara 25, wanda ya yi ta fafutukar ganin ya rika mruza leda a kai-a kai a lokacin jagorancin Jose Mourinho. (Sky Sports)

Kocin West Ham David Moyes bai damu ba game da yarjejeniyar aron dan wasan Manchester United da Ingila Jesse Lingard, mai shekara 28, wacce ba ta ba su damar sayensa ba. (Mail)