You are here: HomeAfricaBBC2021 04 03Article 1223047

BBC Hausa of Saturday, 3 April 2021

Source: BBC

Ana binciken masarautar Kano kan badakalar wasu filaye

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano take gudanar da binciken masarautar Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano take gudanar da binciken masarautar

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano a Najeriya ta ce tana gudanar da binciken masarautar Kano kan badakalar sayar da wasu filaye a unguwannin Gandun Sarki da Dorayi Karama da ke karamar hukumar Gwale.

Shugaban hukumar Muhiyi Magaji Rimin Gado, ya shaida wa BBC cewa tun lokacin sarki na baya hukumar ta hana a sayar da filayen duk da cewa akwai takarda da masarautar ta bayar da dama a yi amfani da wurin domin gudanar da wasu abubuwa da za su kawo ci gaba.

Ya kuma ce "sai da muka hana a sayar saboda muna kan bincike game da filin da ke Darmanawa kuma muna zargi kala-kala a kai a lokacin wancan sarkin, sai muke gani idan muka bar wannan ma to irin abin da ya faru da na Darmanawa zai iya sake faruwa, shi ya sa tun daga wannan lokacin muke sa ido a kan wannan filin."

Muhiyi Magaji ya kuma bayyana cewa akwai lokacin da masarautar ta koka da cewa ana satar wani bangare na filayen ana kuma zuba shara, don haka ta kawo takardar neman izinin cewa za su gina wuraren shakawatawa da wurin wasannni, da kuma ajiyar dawakai.

"To da muka ga cewa wannna ci gaba ne sai muka rubuta wa gwamnati cewa ga abin da suke bukata, gwamnati ta ba da dama ta ce a yi, amma abin mamaki sai kawai aka zo aka ce mana an sayar da filin, sai ya zamana a maimakon a yi abin da aka ce za a yi da shi sai aka sayar," in ji shi.

Shugaban hukumar ya ce batun da ake yanzu haka shi ne kafin ma a sayar da filayen sai aka ce wurin na magada ne, kuma ba a taba samun wani wanda ya taba zuwa fada wa hukumar cewa wurin na magada ba ne, amma yanzu aka ce wurin an yanka wa magada, kuma sun sayar da nasu N575m.

Kana ya ce kuma na masarauta da ya fi na magadan yawa ma sai aka ce an sayar da shi a kan N200m.

"To kuma da muka gayyata sai muka samu labari cewa wasu sun je sun karbi dala dubu dari hudu da goma sha shida da dari shida, wa aka bai wa wadannan daloli, ina aka saka su, me aka yi da su, duk ba mu sani ba," a cewarsa.

Malam Muhiyi ya bayyana cewa da a ce wadanda suka ce sun sayi filin ba su kai su kotu ba wannan labari ba zai fito ba, kuma takardun kotu sai suka nuna cewa hukumar ce ke hana su rawar gaban hantsi.

Ya kara da cewa: "Takardun kotun sun nuna cewa ga wani wanda ya zo wurinmu ya rubuta takarda cewa shi bai ma san an sayar da filin ba amma ga shi ya yarda ya karbi wannan kudi dala dubu dari hudu da goma sha shida a madadin masarauta."

Shin wanene ya bayar da umarni aka sayar da wurin?

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kanon Muhiyi Magaji Rimingado ya ci gaba da yi wa BBC karin bayani cewa binciken nasu ya shafi sanin wanda ya bayar da umarnin sayar da wurin da kuma inda sauran kashi saba'in da biyar bisa dari na kudaden da aka ce an sayar da filin suka shiga.

A cewarsa: "Ai masarautar Kano tana da asusun ajiya na banki, tana da tsari da ka'idoji, abin da muka ce shi ne waye ya bayar da umarni aka sayar da wurin? domin mun yi magana da wasu daga cikin manyan wannan masarauta sun tabbatar mana da cewa ba su ma san an sayar da wurin ba ballantana a ce da su aka yi wannan badakala."

"Mun bukaci masarauta ta ba mu ainihin takardar da ke nuna darajar filin, wane ne ya yi wa filin kudi har ma ya yarda cewa a sayar da shi naira miliyan dari biyu?, tun da mu muna da yakinin cewa ba haka kudinsa yake ba, muna da sahihan bayanan da suka nuna cewa naira miliyan dari bakwai aka sayar da wurin, amma ragowar sun shiga aljihun wasu mutane, a ina suke?," in ji shi.

Shugaban hukumar yaki da cin hancin ya ce abin da hukumar tasa take bukata shi ne a nuna mata takadar darajar filin, kana da kamfani ne ya zo ya duba ya kuma yi wa filin kudi cewa wannan wurin ga yadda za a sayar da shi, sannaa wancan da aka ce na magada ne, hukumar na bukatar su kawo takardun.

"Muna jiran ma'aikatar filaye ta kawo mana takardu, amma kafin nan su ya kamata su kawo mana nasu tun da su suke da'awar wurinsu ne, sannan tun da magana ake yi ta fili da ake tunani na masarauta ne wacce kuma bangare ne na gwamnati, wannan hukuma na da karfin iko a kai," in ji Muhiyi.

Ya kuma ce zargi ya nuna cewa na farko akwai mutum biyu Isa Bayero, da Alhaji Sarki Waziri su suka sayar da wurin amma bisa umarnin mai martaba Sarki.

"Kenan idan bisa umarnin mai martaba Sarki suka sayar mu abin da muka fahimta shi ne babu wannna karfin iko da za a yi haka sannan kudin da aka ce an karba wa aka bai wa? Duk muna da hujjojinmu saboda haka bincike ne zai karkare wadannan baubuwa," a cewarsa.

Shin me masarautar Kano ta ce game da wannan zargi?

Kokarinmu na jin ta bakin masarautar ta Kano ya ci tura, ganin yadda wakilin BBC da ke Kano ya yi ta kiran wayar shugaban ma'aikatan fadar Ahmad Ado Bayero babu amsa.

Kazalika har wannan lokaci bai amsa sakon text da aka aika masa game da batun ba.