You are here: HomeAfricaBBC2021 04 03Article 1222921

BBC Hausa of Saturday, 3 April 2021

Source: BBC

'Yan Najeriya miliyan 51 aka yi wa rajistar NIN

Ministan sadarwa da tattalin arziki na intanet, Dr Isa Pantami Ministan sadarwa da tattalin arziki na intanet, Dr Isa Pantami

Gwamnatin Najeriya ta ce zuwa yanzu an yi wa mutum miliyan 51 rajistar lambar shaidar dan kasa ta NIN.

Ministan sadarwa da tattalin arziki na intanet, Dr Isa Pantami ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN an yi wa mutum miliyan 189 masu wayoyin salula rajistar katin waya wato SIM.

A cewar ministan, miliyan 150 ne kawai daga cikin miliyan 189 suka kammala rajistarsu cikin nasara yayin da ragowar sun samu matsala wajen yin rajistar.

Dr Pantami ya sake yin kira ga 'yan Najeriya a kan su yi rajistar ta lambar shaidar dan kasa kuma ya yi gargadin cewa za a iya yanke musu hukuncin daurin shekara 14 a gidan kaso kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

"Kamar yadda dokar kasa ta tanada, dole ne kowane dan kasa da yan kasashen waje da ke zama a kasar su samu lambar shaidar dan kasa NIN, wadda hukumar tantance yan kasa ta ke gudanarwa. Dokar kasa ta bukaci a yi haka amma mutane da dama sun yi watsi da wannan umarni".

"Babu wata kasa da za ta yi nasara a fannin ilimi da kiwon lafiya da tsara kasafin kudi ko tsarin kasa ba tare da tushen bayanan 'yan kasa ba", a cewarsa.

Ya kuma kara da cewa duk da cewa karbar katin waya na SIM ba dole bane amma. lambar shaidar dan kasa ta zama tilas kuma be kamata ana hada-hadar kudi ko kasuwanci ba tare da NIN ba.