You are here: HomeAfricaBBC2021 04 02Article 1222450

BBC Hausa of Friday, 2 April 2021

Source: BBC

Nijar: Yau Mohamed Bazoum zai sha rantsuwar kama aiki

Sabon shugaban jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum Sabon shugaban jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum

A yau Juma'a ne ake sa ran rantsar da zababben shugaban jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum kan karagar mulki bayan ya lashe zaben da kotun tsarin mulkin kasar ta tababbatar da nasararsa.

Mohamed Bazoum zai karbi rantsuwar kama aikin ce karkashin jagorancin mai shari'a Bouba Mahaman shugaban Kotun Kolin kasar.

Shuwagabanin kasashe da na gwamnati sama da 60 ne ake sa ran za su halarci bikin kuma tuni wasun su suka isa Yamai, babban birnin kasar. Sai dai za a yi bikin karkashin tsauraran matakan tsaro.

Yan kasar na cewa abin alfahari a tarihin dimokradiyyar kasar da shugaban kasa farar hula zai mika mulki ga wani zababben shugaban farar hula.

Daoui Ahmad Baringai, shugaban matasan tarayya ya fada wa BBC cewa abin farin ciki ne zai wakana a wannan rana.

"Abu ne wanda yake da tasiri sosai, shi ne karo na farko tun da aka fara dimokradiyya aka samu wani shugaba zababbe zai ba da akalar jagoancin kasa ga wani shugaban kasa zababbe". in ji Baringai.

A cewarsa, Bazoum mutum ne mai adalci da rikon amana da kuma kishin kasa inda ya bayyana yakinin cewa shugaban zai rike amanar da al'ummar Nijar suka danka masa ta tafiyar da kasar cikin adalci da kyautatawa da kuma neman abin da zai sa kasar ta samu ci gaba.

A cikin watan da ya gabata ne Kotun tsarin mulkin kasar ta Jamhuriyyar Nijar ta tabbatar da Mohamed Bazoum a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar Nijar da aka yi zagaye na biyu.

Mohamed Bazoum na jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya ya ci zaben da kashi 55.66 cikin 100 na kuri'un da aka jefa abin da ke nufin ya zarce tsohon shugaban kasar kuma dan takarar jam'iyyar Tchanji Mahamane Ousmane, wanda ya samu kashi 44.34.