You are here: HomeAfricaBBC2021 04 01Article 1221478

BBC Hausa of Thursday, 1 April 2021

Source: BBC

Kasuwar 'Yan wasa: Cinikin Messi, Pogba, Son, Chiellini, Wijnaldum da Kane

Dan kwallon Manchester United, Paul Pogba Dan kwallon Manchester United, Paul Pogba

Manchester City na cike da burin ganin ta sayo Lionel Messi, mai shekara 33, da kuma dan wasan Borussia Dortmund, Erling Braut Haaland mai shekara 20, dan kasar Norway, don ganin ta kawo su Etihad a bazara, in ji jaridar Sun.

Shi kuwa Paul Pogba ga alama burinsa na barin Manchester United zai iya cika nan kusa a bazaran nan, domin Juventus ta matsu domin ganin ta sake dawo da dan wasan na tsakiya na Faransa, mai shekara 28.

Har ma kungiyar ta Italiya na duba yuwuwar hadawa har da dan wasanta na gaba dan Argentina Paulo Dybala, mai shekara 27, ta bayar don ta karbo Pogban. Kamar yadda Tuttosport ta Italiya ta ruwaito.

Tottenham na ganin abu ne mai wuya ta rabu da tauraron dan wasanta na gaba, na Ingila Harry Kane, mai shekara 27. Kuma ta ce ba ma za ta yi tunanin sayar wa wata kungiyar Premier shi ba, duk da yadda Manchester City and Manchester United ke nuna sha'awar sayensa. Jaridar Manchester Evening News ce ta labarto.

Ita kuwa kungiyar Bayern Munich tana son raba Tottenham din da wasanta na gaba ne Son Heung-min, mai shekara 28, kuma a shirye take ta bi sannu a hankali wajen ganin hakarta ta cimma ruwa ta samun dan wasan na Koriya ta Kudu, wanda sai a bazarar 2023 yarjejeniyar zamansa a Tottenham za ta kare, wanda kuma tuni kungiyar ta London ta kara yi masa sabon tayin kara lokacin zamansa. Football Insider ce ta ruwaito

Har yanzu Chelsea da Manchester United da Juventus da kuma Real Madrid na nan suna fatan ganin sun yi nasarar sayen Golan AC Milan Gianluigi Donnarumma, mai shekara 22,, wanda ya yi watsi da tayi biyu na sabuwar yarjejeniyar zama a kungiyar. Labarin ruwayar Gianluca di Marzio, ta Mail ne.

Ana ganin Barcelona ce za ta yi nasara wajen daukar dan wasan Liverpool Georginio Wijnaldum, mai sheakara 30, wanda zamansa a Anfield zai kare a bazara, amma kuma kungiyar ta Kataloniya na fuskantar kalubale daga Chelsea da Juventus da kuma Paris St-Germain. Sai kuma ita kanta Liverpool din an ce ba ta fitar da ran ci gaba da rike dan wasan na Holland ba, in ji jaridar Marca.

Real Madrid ta yi watsi da bukatar Tottenham bayan da kungiyar ta London ta nuna sha'awarta ta sayen dan bayanta Miguel Gutierrez, mai shekara 19, dan Sifaniya, kamar yadda DefensaCentral, ta ruwaito daga jaridar Star.

Manchester United ta ce a shirye take ta hada da kudi da kuma dan wasanta na Holland Donny van de Beek, mai shekara 23 domin Juventus ta ba ta Adrien Rabiot, mai shekara 25, dan Faransa. Tuttosport, ce ta ruwaito ta jaridar Express)

Dan bayan Italiya Giorgio Chiellini na sha'awar ci gaba da zama a Juventus har gaba da wa'adin yarjejeniyar zamansa, bazarar bana, kamar yadda wakilin dan wasan mai shekara 36, Davide Lippi y ace, to amma har yanzu kungiyar ba ta yi masa tayin wata sabuwar yarjejeniya ba. Ruwayar Sky Italia -ta Italiyanci.