You are here: HomeAfricaBBC2021 04 01Article 1221469

BBC Hausa of Thursday, 1 April 2021

Source: BBC

Ibrahim Zakzaky: Amurka ta zargi Najeriya da yin rufa-rufa a kan kisan almajiransa

Sheikh Ibrahim Zakzaky ne shugaban yan Shi'a a Najeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky ne shugaban yan Shi'a a Najeriya

Wani rahoton Amurka kan batun kare haƙƙin ɗan'adam a Najeriya cikin shekara ta 2020 ya ce har yanzu babu wani ƙarin bayani kan binciken gwamnatin tarayya ko kama wasu da hannu a kashe-kashen da sojojin ƙasar suka yi wa mabiya Shi'a ta Harka Islamiyya ta Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Amurka ta ce kamata ya yi a ce zuwa yanzu Najeriya na da wani ƙarin bayani da za ta iya yi wa duniya a kan zargin da ake yi wa dakarun sojin ƙasar na kisan almajiran Zakzaky kimanin 347, da kuma binne su a manyan kaburbura don boye abin da aka aikata.

Rahoton ya kuma yi dogon sharhi kan take haƙƙin ɗan adam a shekara ta 2020, kama daga kan wanda ake samu a tsakanin jami'an tsaron kasar da kuma kungiyoyin 'yan tada kayar baya.

A wasu bangarorin kuma ya kalli cigaban da aka samu kan kokarin kare hakkin dan adam, ciki har da hukuncin shekara 55 a gidan maza da aka yanke wa wani soja a watan Agusta, bayan kotun soji ta same shi da laifin aikata kisan kai a jihar Zamfara, da ke arewa maso yammacin kasar.

Rahoton ya kuma yi bayani kan ayyukan kungiyoyin masu satar mutane da ya ce sun hallaka mutane da dama a shekara ta 2020.

Ya kuma zargi kungiyar Boko Haram da ISWAP da sace mutane masu yawa a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.

Kazalika ya kuma zargi jami'an tsaro da tsare mutane ba bisa ka'ida ba, da cin zarafin dan adam da azabtar da wadanda ake zargi, inda ya ce akwai kotunan shari'a a jihohi guda goma sha biyu da Abuja, wadanda suna iya yanke hukuncin bulala ko sare hannu ko ma jefewa.

Wani batu kuma da rahoton ya yi duba a kai shi ne na yawan cunkoson ɗaurarru a gidahen yarin Najeriya, da kuma yadda ake ɗaukar munanan dabi'u a cikinsu,

Ya kuma nuna damuwa a kan yadda a wasu gidajen yarin ma babu wani tsari na kula da mata masu dauke da juna biyu, baya ga matsalar rashin isashshen abinci da ruwan sha da mutanen ke fama da ita.

Sa'annan rahoton ya ce duk da bangaren shari'a na da ikon cin gashin kansa a Najeriya, akan samu bangaren zartaswa da yi masa katsalandan domin cimma wasu manufofi na kashin kai, abin da ya saba wa doka.