You are here: HomeAfricaBBC2021 03 31Article 1220383

BBC Hausa of Wednesday, 31 March 2021

Source: BBC

Sonia Mann: Tauraruwar India da ta yi watsi da fina-finan domin goyon bayan manoma masu zanga-zanga

Sonia Mann, a yayin da ta je filin zanga-zanga Sonia Mann, a yayin da ta je filin zanga-zanga

Yawancin fitattun mutane kan rike abin da suke yi da muhimmanci, amma wata 'yar wasan kwaikwayo a Indiya ta sadaukar da kanta da barin sana'arta domin taimaka wa manoma da ke zanga-zanga a kasar.

"Ina shirin daukar wani fim a wannan watan, amma yanzu sun cire ni daga fim din," in ji Sonia Mann a shirin BBC Outlook da ake yadawa ta radiyo.

Tun shekarar 2012 Sonia take sana'ar wasan kwaikwayo, kuma ta fito a fina-finai sama da 12 cikin harsunan Indiya daban-daban.

Fim din da ta fito a baya-bayan nan shi ne "Happy Hardy and Heer" - wanda aka dauki wani bangarensa a biranen London da Scotland - an kuma sake shi a shekarar da ta wuce. Mai yiwuwa shi ne fim dinta na karshe.

Abu ne mai wuya a fadi yadda ake kallon masana'antar Bollywood a Indiya. Amma Sonia ta juya wa "masana'antar fina-finai mafi girma a duniya" baya, wadda ke cike da tarin dukiya da daukaka, da fice fiye da tunanin dan adam.

Amma ta ce ba ta taba yin nadamar daukar matakin ba.

"Shiga zanga-zangar manoman ta sanya ni matukar farin ciki, da nutsuwa fiye da zama tauraruwar fina-finan Bollywood," in ji ta.

Kalubalantar gwamnatin Indiya abu ne mai matukar hatsari ga duk wani dan fim. A baya, taurarin fina-finai da ke sukar lamirin gwamnati na fuskantar turjiyar da kalubalen kin tace fina-finansu kafin fita kasuwa.

Sonia ta san shiga zanga-zangar manoman za ta shafi makomar sana'arta, an kuma gargade ta kada ta nunawa gwamnati yatsa.

Amma duk da haka ta ce ta ji ta gani.

Tsoro

Tun watan Satumbar bara, manoma daga jihohin Indiya daban-daban suka fara taruwa a wajen birnin Delhi domin yin zanga-zangar kin amincewa da matakin gwamnati na sauya doka kan yadda ake noma a kasar.

Firaiminista Narendra Modi da jam'iyyarsa ta BJP sun ce dokar za ta kara wa manoman kudaden shiga. Sai dai manoman sun ce sabanin hakan ne zai faru, tun da sauye-sauyen sun bai wa masu kamfanoni karfin iko.

"Na san cewa bashi ya yi wa yawancin manoman Indiya kanta. Ba sa samun isasshen tallafi daga gwamnati," in ji Sonia.

"Gwamnati ta ce mafi kankantar kudin da ake sayar da buhun masara mai nauyin kilogiram 100 zai kama rufi 1800, kwatankwacin dala 25 (Naira 12,250). Amma rufi 900 zuwa 1000 kadai manoma ke samu 1000."

Manoman na fargabar sabuwar dokar za ta sanya gwamnati ta kawar da mafi kankantar farashin tare da barin 'yan kasuwa yi wa amfanin gonarsu farashi, amma gwamnatin ta ce za ta ci gaba da sanya farashin hatsi da kayan abinci, da rake, da mai da sauransu.

'Kalaman tawaye'

Gwamnati na kokarin dakatar da gangamin tana mai cewa masu zanga-zangar na kokarin yi wa gwamnati tawaye.

Wasu daga cikin ministocin gwamnati na kiran masu zanga-zangar da "Khalistanis" - da ke tunzura mutane da gangan, da tashin hankalin masu dauke da makamai da kokarin dawo da tarzomar da 'yan a-waren Sikh suka yi a shekarun 1980. Yawancin zanga-zangar ta lumana ce, duk da cewa a wasu lokutan an samu taho mu gama da 'yan sanda. Sonia ta ce tana mutunta doka, ta kuma janye daga fito na fito da ake yi.

Daukar mataki kanshaidanu

Wadanda ke sukar masu zanga-zangar sun sanya wa Sonia ido.

"Magoya bayan gwamnati sun yi ta yawo da hotunan da nake sanye da dan kamfai a fina-finaina, tare da kalubalantar tarbiyyarta. Suna cewa ta yaya mace mara da'a za ta wakilci manoma. Sonia na kokarin dauke hankalinta daga kafafen sada zumunta, tana samun nutsuwa daga goyon bayan manoma.

"Tsofaffi na wa su ke kallona a matsayin 'yarsu. Ina ganin bacin rai a idanunsu. Sun amince da ni. Ba zan iya rabuwa da su ba..." in ji Sonia.

Zanga-zangar ta wuce ta ihu da kalaman batanci. Dubban manoma sun kafa sansani a kusa da babbar hanyar shiga birnin Delhi. Anan suke cin abinci, suke kwana. A ranar 1 ga watan Junairu aka tashi da tsananin sanyi.

"Yanayin ba mai kyau ba ne. Akwai tsauri sosai. Mutane da dama na tambayar me ya sa ba za ki koma otal ba? Na ce musu ba zan yi haka ba."

Tantuna

A yanzu kungiyoyin sa-kai sun samar da bandakuna. Sonia na shafe dare da rana da cin abinci a tantunan da aka kafa.

A yanzu kungiyoyin sa kai sun samar da bandakunan wanka da bahaya. Sonia na shafe dare da rana da cin abinci a tantunan da aka kafa.

Kamar sauran masu zanga-zangar, ita ma ta yi girki da wanke-wanke. Tana kuma taimakawa wajen rarrabawa masu zaman dirshan din abubuwan bukatu.

"Na sama wa mata 2,500 wajen kwana, ina ganin ya kamata mata suna bukatar wajen kwana. Na sama musu tantuna, da barguna da abinci. Yanzu da aka shigo bazara, na fara shirin sama musu fankoki."

Burinta ya rushe

Ta sanya kan ta tsundum cikin zanga-zangar, kuma tana fita ne kawai a lokutan da za yi wa magoya baya jawaban karfin gwiwa. Idan tana da lokaci ta kan yi magana a kan abin da ta rasa.

Sonia ta yi fim da shahararrun 'yan wasan Bollywood irinsu, Hrithik Roshan, da suke ba ta kwarin gwiwar sha'awar zama shahararriyar 'yar wasan kwaikwayo.

"Mafarkina shi ne na fito a fim daya da Shahrukh Khan," in ji ta.

A yanzu ta san hakan ba za taba faruwa ba.

'Ni manomiya ce'

Sonia ta girma ne a birnin Amritsar, ta kuma yi karatun digiri a fannin fasahar sadarwa. Kuma jiharta ta Punjab ta shahara wajen samar da biredi. Manoman jihar mabiya addinin Sikhs na sahun gaba a zanga-zangar.
"Na fito daga cikin iyalai manoma. Ina shuka wake a gonata."

Ita ma mabiya addinin Sikh. A ranakun da ba ta da daukar fim, tana zuwa aikin gonarta mai girman eka 10. Duk da haka ba addininta ko waken da ta ke shukawa ne suka sanya ta shiga zanga-zangar ba.

Kwarin gwiwa

Sonia ta ce "juyin juya hali a jini na yake." A watan Satumbar 1990 a lokacin ta na da shekara 16, aka kashe mahaifinta a birnin Amritsar, a kan hanyarsa ta zuwa ganinta a karo na farko.

Baldev Singh Mann na dauke da wasikar da ya rubutawa jaririya Sonia, wadda ta kubuta dag harin da aka kai musu, kuma ita ce ta bata kwarin gwiwa a rayuwa.

"Abar kaunata, ki zamo a sahun gaba domin yaki akan gaskiya. Maharkina shi ne ki tashi bisa tafarkin addinin Sikh, ko Hindu ko Musulunci," mahaifinta ya rubuta a cikin wasikar. "Ki kokarta, ya tabbatar kin daga murya a wajen fadar gaskiya.''

Babu wanda aka kama ko hukuntawa da kisan mahaifinta, dan gwagwarmayar mai kare hakkin manoma da leburori.

Sonia ta sanya an rufo mata wasikar a gilashi, ta makala a gidansu, bayan ta yi kwafin ta, kuma duk inda za ta je tana tare da ita.

"A duk lokacin da na karanta wasikar, sai na ji tamkar ina zaune kusa da shi, ina karanta abin da ke zuciyarsa."

Sonia ta ce a bayyane ta ke mahaifinta ya gyara karya zuwa gaskiya. A shekarar 2019 marubucin littafi kan rayuwar mahaifinta ya tambayi Sonia me ta rubuta game da mahifinta.

Ga abin da ta rubuta.

"Zuwa ga mahaifina, kai ne jagorana, abin alfaharina. Girmamawace kasancewarka mahaifina...ina fatan ka yi alfahari da ni, na kuma cika burinka da ka ke da su akai na, kamar yadda ka rubuta a wasikar da ka min."

An ja daga a yakin

Zanga-zangar ta samu goyon bayan mutane daga sassa daban-daban na kasar. Haka kuma matakin da 'yan sanda suka dauka kan masu zanga-zangar ya sha suka a majalisar dokokin kasashenCanada da Birtaniya.

Gwamnati ta dakatar da kudurin dokar na watanni 18, ta kuma yi tayin a hau teburin sulhu. Sun zo da cikakkun bayanan yadda shirin zai gudana.

"Kowanne kauye a Punjab, da Haryana da Rajasthanzai tura wakilai 20 dan shiga zanga-zangarmu. Bayan kwanaki 20 za a sake tura wasu mutum 20 su maye gurbinsu."

Suna fatan matakin sauya masu zanga-zangar zai ba su damar ci gaba da gwagwarmaya. Sonia ta ce mazauna kauyen sun fusata kwarai, tare da cewa idan sauran iyalan gidaje ba su shiga zanga-zangar ba sauran 'yan kauyen za su daina mu'amala da su.

"Za mu ci gaba da zama anan, dan kwato 'yancinmu, har sai an janye dokar aikin noma baki daya," in ji ta.