You are here: HomeAfricaBBC2021 03 29Article 1218646

BBC Hausa of Monday, 29 March 2021

Source: BBC

Wasika daga Afirka: Kente - Tufafin kasar Ghana da suka shiga fagen tafiyar rangajin yayin tallar kaya kawa

Zayyanar tufafin kente na Virgil Abloh na cikin bukin nuna kayan kawa na Louis Vuitton a Paris Zayyanar tufafin kente na Virgil Abloh na cikin bukin nuna kayan kawa na Louis Vuitton a Paris

A cikin jerin wasikunmu daga 'yan jaridun kasashen Afirka, wata marubuciya, Elizabeth Ohene ta yi la'akari da tashen da yadda tufafin kasarta ke da shi a fadin duniya, a yayin da ake bikin nuna kayan kawa na Louis Vuitton.

Mu a kasar Ghana muna da matukar karfin gwiwa a game da tunaninmu a bangaren kayan ado.

Mun kuma yi amanna cewa tufafi mafi kyau da sha'awa a wannan duniya shi ne sakakken tufafin kente, wanda ko shakka babu na kasar Ghana ne.

Sakakken tufafin ya kasance wata babbar alama ta kasar Ghana da kuma 'yan kasar ta Ghana, har ma kuma da Afirka da duka bakaken fata.

A zamanin da, yadin kente na saraki ne da masarauta kawai, da akan adana su saboda bukukuwa na musamman da kuma manyan mutane a cikin al'ummar kasar Ghana.

A yanzu haka ana samun yadin kente ga kowa a ko ina, amma kuma kyaunsa na nan, kana a duk lokacin da aka saka shi ha yanzu yana da matukar tsada.

Akwai manyan abubuwa da tufafin kente ya kunsa da ke wakiltar kabilu biyu - Ashanti da kuma Ewe (wadanda a cikin su aka fi sanin wannan tufafi da suna kete).

Na amince cewa na kabilun Ewe ya fi kyau, amma zan iya cewa saboda ni da kabilar Ewe ne.

A zahiri, za ka iya gane banbanci tsakanin kente sakar Ashanti da kuma sakar Ewe ba tare da bata lokaci ba.

Adon zanen da ke jikin kente sakar Ashanti su kan zama bai daya kana launukan na fita sosai, yayin da kente sakar Ewe su ka fi kasancewa a wargatse, kana launukan ba su kai na Ashanti haskawa ba.

Amma a yanzu, bayan hada kawuna wuri guda, babu wani banbanci ma yawa tsakanin duka biyun.

Za a iya cewa kente ne idan ya kasance tufafi mai arha ?

Yanzu haka kente ya wuce zama tufafin kwalliya. Ya zama na siayasa, ya kan mika sako, kana yana cigaba da kasancewa kawataccen abu.

Duk da haka, ba za mu iya yanke shawara kan yadda dabi'armu za ta kasance game da kasancewar kente a kasashen duniya.

Muna son shi kuma muna alfahari a duk lokacin da wani babban mutum wanda ba dan kasar Ghana ba ya saka tufafin na kente.

Amma muna matukar damuwa game da tufafin da ake saka wa da yanayin sakar kente a kasar China, wanda ya ke dakushe kaifin tagomashin da yake da shi.

Za a iya kiran shi kente kuwa idan sakar inji ne ba na hannu ba? Na fadi cewa, shin kente ne ida ya kasance tufafi mai arha? Ya kamata a saka shi a kullum a maimakon lokacin bukukuwa na musamman?

Muna ta fama da irin wadannan tambayoyi amma duk da haka muna kallo cikin farin ciki yayin da kente ke samun karbuwa a fadin duniya.

A baya cikin shekarar 2018, kungiyar 'yan majalisun dokokin Amurka sun so su gabatar da wata sanarwa gabanin jawabin tsohon shugaban Amurka Donald Trump kan halin da kungiyar ke ciki, kuma suka rataya zirin kyallen kente a a kan rigunan kwat dinsu.

Haka ya faru; ba su bukaci daukar kwalaye ba.

Zirin yadin kente ya yi nuni da wai babban sako na nuna goyon baya ga kasashen Afirka da aka bayar da rahoton yadda Mr Trump ya yi musu kalaman batanci mako daya kafin nan.

Rataya yadin kente a kan riga kwat

Lokacin bikin nuna kayan kawa da shaharraren mai zayyana kayan ado na Louis Vuitton ya shirya a birnin Paris, kente ya kasance cikin kan gaba a kafafen yada labari a bikin.

Tare da Virgil Abloh a matsayinsa na daraktan shahararren kamfanin zayyane-zayyanen kayan kawa, ba abin mamaki ba ne cewa kente yasamu babbar karbuwa a wurin.

An bayyana Abloh a matsayin mai zayyana kayan kawa na Amurka, amma tun bayan da yana da iyaye 'yan kasar Ghana, mu a kasar Ghana muna daukarsa a matsayin na mu ne.

Ban san ko me masu ruwa da tsaki game da amfani da tufafin kente za su ce game da rataya kente a kan rigar kwat ba, amma kuma ko shakka babu sun kawatar da jama'a a taron bikin nuna kayan kawar.

A kasar Ghana, galibi zanen adon na gargajiya ne, amma akwai matasa masu sana'ar zayyane-zayyanen da ke gwada sabbin hanyoyi na zamani masu launuka da yanayin tufafin.

In baya ga a baya-bayan nan, sarakunan gargajiya ne kawai suke saka tufafin kente. A lokacin bikin hawan dawakai babu abinda za a ka rika gani sai launuka daban-daban na kente da sarakuna suka yi ado da su.

Asantehene, ko kuma sarkin Asante, ya kan samu tufafin na kente babu adadi,kana wata tsayayyiyar doka ita ce muddin aka riga aka yi wa tufafin wani nau'in saka, ba zai yiwu masakan su sake yi wa wni irin wannna sakar ba.

Kente na cigaba da kasancewa a matsayinsa na musamman, komai tsufansa kuwa akan mika wa wasu masu tasowa ne.

Ba ni da tabbaci kan ko me wasu ke yi da tsohon tufafin kente ba, baya ga rayaye wa a dakin jiyar kayan tarihi; ba za ka iya saka wa zuwa shaguna ko ofososhi, ko wurin kallon wasan kwallon kafa ba, komai tsufansa kuwa. Za a rika kallon haka a matsayin kaskantar da yadin.

Ko shakka babu, kente na dada tsufa yana kara daraja ne, ko kuma ana kara darajja shi.

Wannan kasataccen sakakken tufafi na da darajar da aka bayyana a turance a cikin ayyukan marubucin wakokin Turanci John Keats.

Abu mai kyau, abin farin ciki ne na har abada:

Kaunar da ake yi masa karuwa ta ke yi; ba za ta taba gushewa ba.

Ba ka yi cikakken ado mai kyau ba, muddin ba ka daura kente ba.