You are here: HomeAfricaBBC2021 03 29Article 1217911

BBC Hausa of Monday, 29 March 2021

Source: BBC

Shin yadda ake rainon yara a Yammacin Duniya bambarakwai ne?

A wasu al'adu, kwana tare da jariri, wasu lokutan ma a gado ɗaya abu ne da aka saba. A wasu al'adu, kwana tare da jariri, wasu lokutan ma a gado ɗaya abu ne da aka saba.

"Ya fara kwana a ɗakinsa kuwa?" tambaya ce da ake yawan yi wa sabbin iyaye da zarar sun wartsake daga ruguntsimin naƙuda da rayuwa da sabon jariri.

Amma kwana ba tare da jariranmu ba sabon abu ne - kuma ba kowa ne ke yin hakan ba a faɗin duniya. A wasu al'adu, kwana tare da jariri, wasu lokutan ma a gado ɗaya abu ne da aka saba.

Ba wannan ne kawai abin da sabbin iyaye ke yi daban ba a ƙasashen Yamma. Kama daga baccin rana a wani ƙayyadadden lokaci da koya wa yara bacci ba tare da an goya su ko jijjiga su ba da tura yara a keken jarirai, abubuwan da muka saba yi wa yaranmu domin raino ya sha bamban da yadda ake yi a sauran wurare.

Ana bai wa iyaye a Amurka da Birtaniya shawarar kwana a ɗaki ɗaya da jariransu aƙalla tsawon wata shida, amma wasu na ganin wannan a matsayin wani ɗan tsaiko a hanyar jariran ta kwana a dakunansu na daban.

A mafi yawan al'ummomi a faɗin duniya, jarirai na kwana tare da iyayensu na tsawon lokaci. A shekarar 2016, wata bita da aka gudanar kan wani bincike da ya duba yadda iyaye ke kwana da ƴaƴansu a gado ɗaya, ya nuna an fi yin hakan a ƙasashen Asiya: sama da kashi 70 cikin ɗari a Indiya da Indonesia, misali, kuma sama da kashi 80 cikin ɗari a Sri Lanka da Vietnam.

Bincike kan kwana kan gado ɗaya a ƙasashen Afrika ba shi da yawa amma an gano cewa a l'ummomin da ake yi, sababben abu ne.

Debmita Dutta, wata likita a Bangalore, Indiya ta ce duk da tasirin da al'adun Yamma ke yi, har yanzu iyaye na kwana a gado ɗaya da jariransu a Indiya - ko a gidajen da yara ke da ɗakinsu na daban.

"Iyalin da ke da ƴaƴa biyu na da ɗakuna uku, ko wane ɗa na da nasa kuma iyayen na amfani da guda ɗaya, kuma sai ka ga ƴaƴan biyu sun je suna kwana a gadon iyayensu," a cewarta. "Wannan ya zama ruwan dare ."

Kwana a kan gado ɗaya da iyaye hanya ɗaya ce ta rage wahalar da ake sha idan jarirai suka tashi cikin dare, a cewar Dutta. Ita ma ƴarta na da gadonta a kusa da nasu ita da mijnta, inda take kwana har ta kai shekara bakwai. "Ko bayan na daina shayar da ita mama, ta fi son kwana a ɗakinmu," a cewarta.

Ƙarfafa wa yara gwiwa su koyi dogaro da kansu tun suna yara ya yi dai-dai da al'adar ƙasashen Yamma. Saboda haka, kwana tare da yara na sanya wasu mutane su ga kamar shagwaɓa yara ne, kuma hakan zai sa su dogara da iyayensu kan komai.

Amma iyaye masu saɓanin ra'ayi kamar Dutta ba su yarda da haka ba. "Kana iya koya masu ra'ayin kansu, da kansu za su zame jiki daga gare ka," a cewarta. "Ba za su maƙale maka ba har abada."

Iyaye da dama a al'ummomin Yamma na koya wa ƴaƴansu yin bacci ba tare da an goya su ko jijjiga su ba. Takan kai ma suna barin jariri shi kaɗai ya yi kuka ya "ƙoshi" duk domin bacci ya ɗauke shi tsawon lokaci, domin iyayen su samu su huta.

A Austreliya, akwai makarantun gwamnati da iyaye ke iya kai ƴaƴansu a koya musu bacci da kansu ba tare da an lallaɓe su ba.

Al'adu na shafar yadda jarirai ke bacci da inda su ke bacci da yawan baccin da suke yi.

A binciken da Jun Kohyama na cibiyar lafiya ta Tokyo Bay Urayasu Ichikawa ya gudanar, an gano cewa jarirai a Japan ba su cika baccin rana ba idan aka haɗa da sauran ƙasashen Asiya da zarar sun kai wata uku da haihuwa, wataƙila saboda a al'adar Japan, bacci ragwanci ne.

Kohyama ya gano cewa yara a ƙasashen Asiya ba sa bacci da wuri idan aka kwatanta da takwarorinsu na ƙasashen Turai. Yana ganin wannan ba ya rasa nasaba da yadda iyaye ke son zama cikin ƴaƴansu da yammaci.

Kwana kan gado ɗaya da yara abu ne da aka saba a al'adance a Japan, kuma wannan na iya zama ɗaya daga cikin dalilan.

"Iyaye na ganin jaririnsu wani ɓangare ne na jikinsu," a cewarsa.

Duk da cewa a Birtaniya da Amurka, likitocin yara na bai wa iyaye shawarar kwana tare da ƴaƴansu don rage haɗarin cutar SIDS ta mutuwar farat ɗaya a jarirai, suna kuma gargaɗin kwana a gado ɗaya da jariri saboda hakan na ƙara haɗarin gamuwa da cutar ta SIDS.

Amma Rashmi Das, wani farfesa a ɓangaren lafiyar yara a Indiya ta ce rashin isasshen bincike kan wannan batun ne ya sa zai yi wuya a iya ganewa idan kwana a gado ɗaya na ƙara haɗarin kamuwa da SIDS idan aka ɗauke sauran abubuwan da ke iya haifar da shi kamar shan taba da shan barasa.

Bincike kan batun SIDS na yawan fitowa ne daga ƙasashe masu arziƙi, inda ba a fiye kwana a gaɗo ɗaya ba. Amma a ƙasashe masu karancin arziƙi, inda kwana da jariri al'ada ce, ba a fiye ganin jarirai na mutuwa dalilin SIDS ba.

Idan wani da ke rayuwa a Yamma ya ɗauko al'adar inda ya fito a ko ina a faɗin duniya, lallai zai zo da ƙarancin hadarin SIDS. Iyali daga Pakistan da ke zama a Birtaniya, misali, na da ƙarancin haɗarin SIDS fiye da iyalai ƴan Birtaniya - duk da iyaye mata na kawana tare da jariransu.

"Al'adun ne ke da alaƙa da ƙarancin SIDS," a cewar Helen Ball, farfesa kan tarihin al'adun gargajiya a Jami'ar Durham kuma darakta a ɗakin gwajin yadda iyaye da ƴaƴansu ke bacci na jami'ar.

Iyaye mata ƴan asalin Pakistan a yankin Bradford a Birtaniya sun fi shayar da jariransu mama kuma ba su fiye shan taba da barasa ba. Haka kuma, ba su fiye barin jariransu su kwana a wani ɗaki daban da nasu ba - kuma duka waɗannan abubuwan ne da aka san suna haifar da SIDS.

Das ya ce zai so ya ga ana ƙarfafa wa iyaye gwiwa su riƙa kwana da jariransu a gado daya amma a yi wa gargaɗin ban da shan taba da barasa kuma kar su zama masu teɓa". Ƙungiyar The Lullaby Trust mai son kare SIDS a Birtaniya ta bai wa iyaye shawara idan suna so su riƙa kwana da jariransu.

Kamar yadda kwana tare ke sa kusanci da dare, goya jariri na samar da hanyar kusanci da rana a lokacin da iyaye ke ayyukansu na yau da kullum a cikin gida.

Maimakon wani sabon salo, goya jariri wani abu ne da mutane suka daɗe suna yi.

Sai da keken tura jarirai ya shahara ne aka fara daina goya jarirai a wasu ɓangarorin ƙasashen Yamma.

A sauran ƙasashen duniya, akwai hanyoyi da dama na ɗaukar jarirai.

Ko iyayen da ba sa goyo za su lura cewa ɗaukar jarira a ɗan yi kaiwa da komowa da su ka sa su nutsu. "Suna sanin cewa wannan motsin na kwantar wa jariri hankali," a cewa Kumi Kuroda ta cibiyar Riken Centre a Japan.

Kuroda ta fara duba yadda ɗaukar jarirai ke shafar jikin yara lokacin da ta ga wani bincike da aka yi a baya, wanda aka gaza gano alaƙa tsakanin yawan lokacin da aka ɗauki jarirai da yawan kukansu. "Sai na gaza yarda da hakan," a cewarta.

Bincikenta ya gano cewa ɗaukar jariri na rage bugawar zuciyarsu da yawan motsa jikinsu da yawan kukansu.

Ta ce da ta ci gaba da bicike ta gano cewa yin motsi da jariri ba tare da ɗaukarsa ba kamar a cikin kekensa ko kujerar jarirai ta mota, da kuma ɗaukar jaririn a hannu ba tare da an motsa ba, duk suna kwantar wa jariri hankali amma sun fi aiki idan aka yi su tare.

Zama kusa da jariri, da rana da dare, shi jarirai ke buƙata don haka aka halicce su.

A watanninsu na farko a duniya, suna buƙatar a yawaita ba su abinci. Ko a lokacin da jikinsu ya fara auna lokutan bacci da tashi kuma suka fara bacci sosai da dare, farkawa cikin dare a shekararsu ta farko ba abin damuwa ba ne.

Amma dangi da abokai ba sa gaya wa sabbin iyaye a ƙasashen Yamma cewa babu damuwa don jaririnsu na farkawa daga baccin dare. "Mun camfa wa kanmu cewa bai dace jarirai su riƙa tashi cikin dare ba," a cewar Ball.

Wannan camfi na da matsala. Gutsire bacci a farko-farkon jego na iya janyo cutar tsananin damuwa ta bayan haihuwa. Amma Ball ta ce ƙoƙarin 'gyara wa' jariri baccin ba zai yi maganin matsalar ba - illa ma dai tallafa wa iyaye ta hanyar da ya kamata na iya taimaka wa lafiyar ƙwaƙwalwarsu.

"Iyayen da ke da cutar damuwa na ganin gutsire baccin iyaye da jarirai ke yi ya fi taɓa iyaye masu cutar damuwa," a cewarta. "Abin da ya sa muka ce haka shi ne, ya kamata mu gyara abin da ke faruwa a ƙwaƙwalwar iyayen, mu ba su tallafi."

Tunanin da ake yi na cewa jarirai da suka ɗan fara girma ya kamata su yi bacci tun daga dare har gari ya waye ya fito ne daga wani bincike da aka yi a 1950 da aka gano cewa, a cikin jarirai 160 da ke rayuwa a Landan, kashi 70 cikin 100 sun fara bacci ba tare da farkawa cikin dare ba a lokacin da suka kai wata uku da haihuwa.

Amma masu binciken sun bayyana "bacci ba tare da farkawa ba" a matsayin rashin tashin iyayensu ta hanyar yin kuka ko rigima tsakanin ƙarfe sha biyu na dare zuwa ƙarfe 5 na asubahi - duk da haka dai bai kai awa 8 da iyaye ku buƙata ba.

Kashi 30 cikin 100 na jarirai ba su fara daɗewa suna bacci ba da dare a wannan shekarun, kuma rabin jariran da ke "baccin ba tare da farkawa ba" sun koma suna farkawa sau da dama da dare a shekararsu ta farko.

Jikin jarirai bai sauya sosai ba a shekarun da suka gabata," a cewar Ball.

"Amma al'adarmu ta sauya sosai, kuma zatonmu a kan jarirai da raino ya sauya sosai a ƴan shekarun da suka gaba."

Ko a yau, bincike da dama da ake yi kan baccin jarirai na duba wani rukuni na wasu al'ummomin duniya ne. Mafi yawan binciken da aka gudanar a shekarun da suka gabata an yi ne a kan jariran ƙasashen Yamma," a cewar Ball.

Yayin da akwai bambanci a tsakanin al'adu idan aka zo batun yadda muke rainon jarirai, akwai banbanci a cikin hakan ma. Ba kowa ne a Yamma ke ganin ya dace a bar jariri ya kwana shi kaɗai ba. A wani bincike, misali, iyaye ƴan Italiya na ganin rashin "kirki ne".

Yadda mutum ke gudanar da rayuwarsa na taka muhimmiyar rawa kan yadda mutane ke rainon jariransu, kuma ko wace uwa ko uba na lalubo hanyoyin gudanar da abubuwansa, a cewar Kuroda.