You are here: HomeAfricaBBC2021 03 26Article 1215691

BBC Hausa of Friday, 26 March 2021

Source: BBC

Farautar giwaye da ake yi ta sa dabbobin na ƙarewa a Afirka

A yanzu giwayen Afirka na fuskantar barazanar ƙarewa A yanzu giwayen Afirka na fuskantar barazanar ƙarewa

Kasuwancin hauren giwa da asarar halittu masu muhimmanci da sake fahimtar yanayin yadda tsarin halittar giwa yake, sun bankaɗo yadda a baya aka raina barazanar da giwayen Afirka ke fuskanta.

A yanzu giwayen Afirka na fuskantar barazanar ƙarewa, kamar yadda wani bincike na Hukumar Kula da Dabbobi da Muhalli ta Duniya IUCN ya bayyana.

Su ma giwayen da ake samu a yankin Savanna suna fuskantar ƙarewa.

Raguwar da suke yi cikin gomman shekaru sun sa dabbobin sun faɗa cikin rukunin na'ukan da ke barazanar ƙarewa a ban ƙasa.

Akwai wasu nau'in giwaye da a baya IUCN ta sanya su a jerin waɗanda ke barazanar ƙarewa.

IUCN ta yi ƙiyasin cewa giwaye 415,000 ne suka yi saura a Afirka.

Amma yawan giwayen ya ragu da fiye da kashi 86 cikin 100 cikin shekaru 30 da suka gabata. Yayin da yawan giwayen da ake samu a yankin savanna ya ragu da a kalla kashi 60 cikin 100 cikin shekara 50.

Yanayin ya danganta daga ƙasa zuwa wata ƙasar. A Botswana alal misali, ana ganin akwai giwaye da yawa da yanayin ƙasar wajen bai karɓi yanayin jikinsu ba. Amma idan aka yi la'akari da baki ɗaya nahiyar, to lallai giwayen ƙarewa suke yi.

Dr Ben Okita, wanda ke jagorantar sashen kula da giwaye na hukumar IUCN, ya ce binciken na baya-bayan nan abin ɗaga hankali ne.

Ya shaida wa BBC News cewa har yanzu kasuwancin hauren giwaye na daga cikin manyan dalilan da ke jawo raguwar dabbobin.

"Yana ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke jawo hakan," a cewarsa.

"Amma akwai wani babban abin kuma da ke yi musu kisan gilla da ke buƙatar a mayar da hankali sosai wajen magance shi - wato abubuwan da ke lalata albarkar ƙasa kamar sare bishiyoyi da ke jawo musu rashin abinci.

"Babban ƙalubale ne ga dabbobin da ke buƙatar manyan yankuna kuma suke doguwar tafiya.

"Su dabbobin daji ba su san iyakokin ƙasa da ƙasa ba.

"Don haka idan har muna son sauya abubuwa to dole muna buƙatar hadin kan masu iko da iyakokin nan don tsara yadda za a yi amfani da filin yadda ya kamata.

Dr Okita ya bayyana cewa a duk inda dabbobi ke amfani da waɗannan filaye, to yana da muhimmanci a inganta musu shi yadda za su ji daɗin amfani da shi.

"Na san gwamnatocin Afirka na son yin hakan tare da al'ummomin da ke zaune a kusa da inda dabbobin suke," a cewar Dr Okita.

"Don haka kawai muna buƙatar a yi hakan.

"Ina da kyakkyawan fata, cewa za mu iya sauya abubuwa."