BBC Hausa of Sunday, 14 March 2021

Source: BBC

Lafiya Zinariya: Dalilan da ke sa mace ta haifi ɗa ba rai

Najeriya ita ce kasa ta uku a cikin jerin kasashe shida da aka fi samun mace-macen jariran a duniya Najeriya ita ce kasa ta uku a cikin jerin kasashe shida da aka fi samun mace-macen jariran a duniya

Najeriya ita ce kasa ta uku a cikin jerin kasashe shida da aka fi samun mace-macen jariran a duniya. Kasar Indiya ce ta farko, sai Pakistan ke biye da ita.

Ragowar kasashe ukun kuma su ne Jamhuriyar demokradiyyar Congo, sai China, sannan Habasha wato Ethiopia. Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata makala da aka wallafa a shafin intanet na hukumar lafiya ta Duniya.

Makalar da aka wallafa a shekarar 2019 ta bayyana cewa, kimanin 'yan tayi miliyan biyu ne ke mutuwa duk shekara daga shekarar 2000 zuwa ta 2019.A cewar makalar asarar da aka samu ta bambanta daga wani bangare zuwa wani a duniya.

Inda matsalar ta fi kamari a yankin kudu da hamadar saharar Afrika. Sai kuma kudancin Asiya. A cewar makalar, a cikin kasa guda ma ana samun wasu wuraren da suka fi wasu, samun matsalar ta matan da ke haihuwar jarirai ba rai.

Kamar misali a yankunan karkara a kudancin kasar Nepal, inda yawancin mata suka fi haihuwa a gida ba tare da kwararriyar ungozoma ba, mace-macen jariran ya kai kashi 30 zuwa hamsin cikin dari sama da abin da ake samu a biranen kasar.

Hakazalika, matsalar ta rubanya a yankunan karkara da ke yammacin kasar Sin, idan aka kwatanta da abin da ake samu a kasar gaba daya. Dalilan da ke janyo wadannan bambance-bambance a cikin kasa daya kuwa, inji makalar sun hada da rashin samun damar yin awon ciki da karbar haihuwa mai inganci.

Da rashin kyakkyawan tsarin tura mai ciki babban asibiti a lokacin da ya dace da kuma rashin samun yin tiyata domin a cire da. Masu makalar sun ce samar da abubuwan da ake bukata da kuma cin gajiyar jarin da ake zubawa don magance matsalar, zai taimaka gaya wajen kare aukuwar haihuwar jarirai ba rai, a wadannan yankunan da matsalar ta fi muni.

Makalar ta kuma yi karin bayani kan yadda ake ci gaba da samun wannan matsalar a tsakanin wasu mutane a kasashe masu karfin kudaden shiga.Inda ta ce kabilu marasa rinjaye a kasar Canada ba sa samun kula sosai a yayin da matansu ke da ciki, lamarin da ke janyo karuwar mutuwar jarirai a wajen haihuwa.

Haka kuma mata bakaken fata Amurkawa, sun fi fuskantar barazanar haihuwar jarirai ba rai har sau biyu, idan aka kwatanta da mata Amurkawa fararen fata.

Makalar ta kuma kara da cewa zurfin ilimin mace shi ma yana tasiri wajen bambanci da ake samu, abin da ke janyo haihuwar jarirai ba rai a kasashen da ke da karfin kudin shiga.